Daga Mohammad A. Isa, Katsina.
An bayyana kungiyar nan ta kungiyar ‘Ladon Alkhairi’ a matsayin kungiyar da ta zarta tsararrakinta na jam’iyya PDP a matakin jiha har ma da kasa baki daya wajen aiki tukuru tare da zabaro ‘ya’yan kungiyoyin jam’iyyun siyasa daban-daban zuwa jam’iyyar adawa ta PDP.
Shugaban kungiyar tallata ‘yan takarar jam’iyyar PDP na kasa ‘PDP National Youth Vanguard’ na Jihar Katsina, Alhaji Umar Misbahu Mai Zare ne ya bayyana haka a yayin da yake jawabi a taron hadin gwiwa tsakanin kungiyar PDP National Youth Vanguard da ta Ladon Alheri a Katsina a ranar Lahadin nan.
Mai zare ya bayyana cewar, ba a jam’iyyar PDP ba kadai ba ma, ko a jam’iyyar da suke adawa da ita ta APC, ba su da jajirtattar kungiya kamar kungiyar Ladon Alkhairi ce, a wajen fafutika da yin aikin tukuru ba dare ba rana wajen zabaro al’umma zuwa jam’iyyarsu ta PDP da kuma ci gabantar da jam’iyyar a fadin jihar Katsina.
“A duk cikin kungiyoyin da muke da su na jam’iyyar PDP na jihar Katsina kai har ma da APC din, babu masu yin aiki tukuru kamar ta(Ladon Alkhairi).” In ji shi
“Domin (Kungiyar Ladon Alkhairi) suna shiga ko’ina domin su tabbatar da dan takararmu na gwamna ya kai ga gaci.” Ya yabe ta.
Alhaji Misbahu mai zare har wayau, ya bayyana kurgiyar Ladon Alkhairin a matsayin PDPn Alkhairi, ba wai ta iya kadai a Ladon Alkhairi ba.
“Kuma mun san in sun yi tallar Lado, to sun yi tallar Atiku da duk ‘yan takararmu. Saboda su ba kungiyar ladon alkhairi kawai ce ba, kungiyar PDPn alhairi ce!” Ya jaddada.