Wata kotun Majistare da ke Yaba a yau Juma’a ta bayar da umarnin tsare wani ɗan sanda, ASP Drambi Vandi, wanda ake zargi da harbe wata Lauya da ke Legas, Bolanle Raheem, a ranar Kirsimeti.
Babban Alkalin Kotun, C.A. Adedayo, ya ba da umarnin a ajiye wanda ake zargin a gidan yari na Ikoyi har zuwa lokacin da daraktan shigar da kara na jihar, DPP ya ba da shawarar mataki na gaba.
Ta kara da cewa umarnin da aka bayar na tsawon kwanaki 30 ne na farko kafin a gudanar da binciken ƴan sanda kan lamarin.
Ta ba da umarnin a kwafi fayal ɗin shari’ar a aika zuwa ga DPP don neman shawara.
Adedayo ta ɗage ci gaba da sauraron karar har zuwa ranar 30 ga watan Janairu domin sake duba umarnin ajiye wanda ake zargin a gidan yari da kuma shawarar DPP.