Jam’iyyar APC ta ce jiga-jiganta sun yi nasarar dinke wata baraka da batun hada gangamin yakin neman zabe na dan takararta na shugaban kasa ya haddasa.
A kwanakin baya ne wani jerin sunaye da aka kwarmata a kafofin sada zumunta da sunan cewa shi ne gangamin yakin neman zabe na dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu, lamarin da rahotanni ke cewa bai yi wa shugabannin jam’iyyar da wasu gwamnoninta dadi ba.
Amma bayan wani dogon zama da gwamnonin APC da ‘yan kwamitin gudanawarta da kuma shugabannin gangamin yakin neman zaben, jiga-jiganta sun ce sun cimma maslaha.
Shugaban kungiyar gwamnonin APC, kuma gwamnan jihar Kebbi, Alhaji Atiku Bagudu ya shaida wa BBC cewa sun shawo kan matsalar:
”Da ma wani kuskure aka yi, wato wani ma’aikaci ne ya fitar da jerin sunayen ‘yan kwamitin yakin neman zaben kafin a kammala hadawa. Ka san ana hada sunayen ne ana tuntuba. Amma yanzu an samu fahinta. Da ma ba baraka ba ce. Kuma dukkan mu muna jaddada goyon bayan ga shugabannin jam’iyyarmu da dan takaranmu na shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.”