• About us
  • Advertise
  • Privacy Policy
  • Contact
Monday, January 30, 2023
  • Login
Katsina City News
Advertisement
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta
No Result
View All Result
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta
No Result
View All Result
Katsina City News
No Result
View All Result
Home Sashen Hausa

An ƙaddamar da Ƙungiyar Tsangaya a Katsina 

December 24, 2022
in Sashen Hausa
0
An ƙaddamar da Ƙungiyar Tsangaya a Katsina 
0
SHARES
38
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Zaharaddeen Ishaq Abubakar @ Katsina City News

A Ranar Asabar 24 ga watan Disamba gamayyar mahardata Alqur’ani da Malaman Tsangayu (Makarantun Allo) Ƙarƙashin Jagorancin Alaramma Malam Masa’udu Rafin daɗi, suka kaddamar da Ƙungiyar Malaman Makarantun Allo da Mahardata Alqur’ani ta jihar Katsina.

Ƙungiyar da take da wakilai a dukkanin ƙananan hukumomi 34 na jihar Katsina ta gudanar da taronta a Unguwar Malali a garin Katsina. 

Da yake bayyana Dalilan kafa wannan kungiyar a jihar Katsina, Sakataren ta Alaramma Dahiru Tijjani (Saalbarka) yace “Halin da Makarantun Allo suke ciki da Almajirai yasa mukaga dacewar samar da wata kungiya mai murya daya da zata taimaki ‘Yan’uwanmu Almajirai, da samar masu yanayi mai kyau mai inganci da zasu rayu a ciki.”

Yace akwai kungiyoyi da ake cewa na Tsangayu da akace suna da alaƙa da Gwamnati kuma suna Tallafawa makarantun tsangayu, amma mu mune makaranta kuma muke tare da Almajirai amma bamu taba sani ko ganin wani tallafi da akace ana yi ba.” Yace saboda haka muka samar da wannan Ƙungiya da zamu kasance yamu-yamu mu ga abinda zamu iya yi don samar da tsari ga Almajirai, sana kuma ga masu iya shiga kungiyar don tallafawa da inganta makarantun Allon kofarmu buɗe take.” Injishi.

Alhaji Sabo Musa mai bawa Gwamnan Katsina shawara na musamman akan tsare-tsare da maido da komai a muhallinsa, ya halarci taron inda yayi tsokaci da wa’azi jan hankali akan dukkanin bangarorin Al’umma Iyayen da ke turo yaransu don karatun Alkur’ani, malaman, masu hannu da shuni da ita kanta Gwamnati.

S.A Sabo Musa ya ce “da fari muji tsoron Allah, Alqur’ani ba abin wasa bane ba abin rainawa bane.” Yace sai kuga Iyayen yara sun kashe maƙudan kuɗi wajen kai ‘ya’yansu makarantar Boko, amma sun kai ‘ya’yansu makarantar Allo ba tare da wata kulawa ba. Yace sana masu kudi yakamata suma suji tsoron Allah su taimaki makarantun Allo da iya abinda zasu iya yara na cikin mawuyacin hali bama kamar yanzu lokacin sanyi da inda yara zasu kwanta ma a takure suke.

Yace, muna kira ga ita wannan ƙungiya da ta yi kokari ta samar da tsari mai kyau yace shi zai jagoranceta ta shiga Gwamnati don samun duk irin gudummawar da suke bukata, yace koda Abubuwa sunyiwa Gwamnati yawa amma zata iya shiga ciki don Tallafawa Kungiyar.

Tsohon mai bawa Gwamnan jihar Katsina shawara akan Makarantun Allo, Malam Lawal Mani Gambarawa, ya bayyana gamsuwa akan wannan ƙungiya sana kuma yayi kira ga Gwamnatin Aminu Bello Masari da ta Tallafawa makarantun Allo ta hannun da ya dace, yace yakamata ta maido da tsarin can na Gwamnatin baya domin tsari ne mai kyau. Babban Baƙo a wajen, kuma shugaban tsangaya na ƙasa Asshiekh Ambasada Sayyid Hassan, ya bayyana irin shuge da fice da sukayi a mataki na ƙasa don tabbatar da al’amarin makarantun tsangayu sun zama masu cin gashin kansu.

Yace da yardar Allah kamar yanda ake warewa ko wace ma’aikata kudi a wajen Budget haka za’a samar da ma’aikatar harkokin tsangayu kuma a dunga ware masu kudaden su, yace yanzu haka a majalisar Wakilai anyiwa tsarin Karatu na ɗaya anyi ba biyu. 

Ambasada Sayyid Hassan yace lallai idan ka samar da wannan ma’aikata Almajiri zai samu gata. Yace daga cikin kokarin da suke na ganin Almajirai sun samu gata hadda tuntubar ƙasashe da zasu iya bada tallafi domin hana Almajiran barace barace. Yace a yanzu zamu iyacewa hakarmu ta fara cimma ruwa, saboda daga wannan sabuwar shekara zamu fara samun tallafi daga ƙasashen waje, inda zamu Tantance makarantun Allo, mu basu Fom su cike a bude masu Asusun ajiya inda ko wane Almajiri zai dunga samun akalla dubu takwas a wata, kuma ko sunkai sunawa.

Sana yayi kira ga Gwamnatin jihar Katsina da ta taimaka ta samar ma wannan kungiya mazauni na Dindindin da Motar Zirga-zirga domin Sauƙaƙa Ayyuka.

Tun da farko Shugaban kungiyar, Alaramma Malam Masa’udu Rafin daɗi yayi Godiya ga dukkanin mahalarta taron gami da kira ga dukkanin Alarammo da su shiga kungiyar da zuciya daya kuma su tsarkake zukatan su, yace “Lallai mu muna yi ne da kyakkyawar niyya kuma zuciyarmu a bude, kuma zamu shiga duk inda ya dace domin nemo abinda ya dace don tallafawa ita wannan kungiyar.

Taron ya tattaro wakilan kananan hukumomi 34 da baki daga ko ina a fadin jihar Katsina, da mai bawa Gwamnan jihar Katsina shawara akan dawo da komai bisa tsari, Alh. Sabo Musa, tsohon mai bawa Gwamnan Katsina Shema shawara akan Almajirai Malam Lawal Mani, Alarammomi da Shugaban Tsangaya na kasa Ambassador Sayyid Hassan daga Kano.

Share

Related

Source: Katsina City News
Via: Katsina City News
Previous Post

Gwamnatin Kano ta kulle masallatai da makarantar Abduljabbar bisa bin umarnin kotu

Next Post

Reports  on Katsina National Talenta Hunt Challenge 2022

Next Post
Reports  on Katsina National Talenta Hunt Challenge 2022

Reports  on Katsina National Talenta Hunt Challenge 2022

Recent Posts

  • APC ta gano kafafen yada labaran da PDP ke ɗaukar nauyi su yaɗa karya a kan Tinubu
  • Emefiele: We’ve collected N1.9trn old naira notes so far — N900bn more to go
  • Hanyoyi Shida Domin Kiyaye Basir Cikin Sauƙi.
  • Bankin CBN Ya Samar Da Naira Miliyan 120 Domin Yin Canjin Kudi A Katsina.
  • INEC ta kara tsawaita wa’adin karbar katin zabe

Recent Comments

No comments to show.

Archives

  • January 2023
  • December 2022
  • November 2022
  • October 2022
  • September 2022
  • August 2022
  • July 2022

Categories

  • Biography
  • City News
  • Condolence
  • Fasahar zamani
  • Featured
  • General Stories
  • History
  • Kula da Lafiya
  • Labaran Fim
  • Literature
  • News and Analysis
  • News and Reports
  • Photo News
  • Rubutu da Marubuta
  • Sashen Hausa
  • Tarihin Kasar Katsina

Browse by Category

  • Biography
  • City News
  • Condolence
  • Fasahar zamani
  • Featured
  • General Stories
  • History
  • Kula da Lafiya
  • Labaran Fim
  • Literature
  • News and Analysis
  • News and Reports
  • Photo News
  • Rubutu da Marubuta
  • Sashen Hausa
  • Tarihin Kasar Katsina
  • About us
  • Advertise
  • Privacy Policy
  • Contact

No Result
View All Result
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In