Tuƙa keke hanyar sufuri ce da ta shafe tsawon ƙarni biyu ana damawa da ita a jerin hanyoyin sufuri saboda sauƙin sufuri, sauƙin kula da kuma araha.
Tuƙa keke hanya ce ta motsa jiki kamar yadda ƙudirin Hukumar Lafiya ta Duniya kan motsa jiki na zangon 2018 — 2030 ya yi nuni da tasirin motsa jiki ga lafiya, tattalin arziƙi da walwalar al’umma. Kuma ƙudirin ya zaburar da yunƙurin mahukunta na samar da tsarika da za su yi wa mutane ƙaimi kan motsa jiki, wanda hakan zai taimaka wajen cimma ɗaya daga cikin Muradun Cigaba Mai Ɗorewa na Majalisar Ɗinkin Duniya.
Har wa yau, keke na da amfani ga lafiya da muhalli kamar haka:
- Hanya ce ta yin matsakaicin motsa jiki / atisaye. Kuma motsa jiki hanya ce ta rage haɗarin kamuwa da larurori kamar ƙiba, ciwon siga, hawan jini, ciwon zuciya da kuma ciwon daji/kansa.
- Har wa yau, tuƙa keke na iya kiyayewa ko kuma rage haɗarin ciwon gwiwa.
- Keke ba ya fitar da iskar makamashi da ke gurɓata iska. Saboda haka, amfani da keke na bunƙasa aikin huhu tare da rage haɗarin kamuwa da cutukan huhu ko numfashi.
- Amfani da keke na rage barazanar ɗumamar yanayi ga duniyarmu, saboda keke ba ya fitar da gurɓatacciyar iskar makamashi.
- Keke hanyar sufuri ce da ke da ƙarancin haɗari saboda sauƙin sarrafuwa yayin tuƙi.
- Dacewa da tattalin arziƙi saboda babu buƙatar sayen fetur ko gas, sannan kula ko gyaransa na da sauƙi sosai.
Source:
©Physiotherapy Hausa
Via:
Zaharadeen