
Hon Musa Yusuf Gafai ya bayyana cewa “Kungiyar Ladon Alkhairi bata taɓa tafiya da wanda bashi a Katin zaɓe, idan ka shigo kungiyar Ladon Alkhairi ba tare da Katin zaɓe ba to baka da muhalli a cikinta” Gafai ya bayyana haka ne a lokacin da Kungiyar Yaƙin neman zaɓen Sanata Babba Kaita a matsayin Sanata, na Shiyyar Daura mai suna “Ahamadiyya Alkhairi” ta ziyarce shi, domin tattauna wasu batutuwa da zasu kawo cigaba da nasara a zaben 2023 dake ƙaratowa.
Hon. Mubarak Isah Mani shine shugaban kungiyar Ahamadiyya Alkhairi wadda yace a ƙarƙashin kungiyar akwai fiye da kungiyoyi ɗari biyar da suke mara mata baya domin tabbatar da nasarar Ahamed Babba Kaita.
Da take jawabi a wajen taron shugabar matan kungiyar Ladon Alkhairi Hajiya Yahanasu Muhammad ta bayya cewa “Babba Kaita Uban Talakawa ne, wanda ba’a taba samun wani sanata da yake kawo cigaba kai tsaye ga talakwa kamarsa ba.” Shima Sakataren Kungiyar Ladon Alkhairi Hon. Abubakar ‘Yantaba yace “Abin kunya ne ace wai wani ya fito takara daga Shiyyar Daura, tare da Sanata Babba Kaita,” yace ko da yake jam’iyyar APC ba Al’umma bace gabanta shiyasa har take ganin akwai wani wanda yafi Babba kaita a cikinta, amma ba don haka ba ai duk mai kishin al’umma ko daga wace jam’iyya ya fito zai goyi bayan takarar Sanata Babba Kaita.” Ya bayyana
Tun da fari Hon Musa Gafai ya bayyana jin dadinsa da ziyarar ta kungiyar Ahamadiyya Alkhairi inda ya sha Alwashin tafiya dasu ƙafa da ƙafa duk inda zasu shiga yakin neman zabe yace da yanzu da bayan anci zaɓe suna tare da Kungiyar kuma suna tare da Sanata Babba Kaita saboda mutum ne mai ilimi da Dattako. Taron ya gudana a Dakin taro na Gafai Restaurant dake kan Titin kofar kaura cikin garin Katsina a ranar Asabar, inda ya hada wakilan Kungiyar ta Ahamadiyya Alkhairi daga Shiyyar Daura, da kuma Shugabannin Kungiyar Ladon Alkhairi na jihar Katsina da ‘Yan jarida.