@Katsina City News
Wani yaro mai suna Ahmad Ali Ilu kurfi Dan shekaru Goma sha shidda ya ciri tuta a walimar saukar karatun alkur ani mai tsarki. da makarantar Zainab memorial academy tayi a ranar Asabar 6 ga watan Mayu 2023.
Walimar ta saukar karatun Wanda akayi shi a harabar makarantar dake bayan Nysc camp dake titin hanyar zuwa Mani a katsina.
Walimar ta samu halartar Masana karatun Alkur ani mai tsarki daga jahar katsina.
Ya kuma samu halartar Manyan baki da uwayen dalibai da yan uwansu da abokan arziki.
Daga cikin daliban da suka Ciri tuta har da wani mai suna Ahmad s Salis Wanda karatun shi ya burge kowa a mahalarta taro.
Walimar na yaye daliban ana yinshi lokaci lokaci don karfafa gwaiwa ga daliban don su kara dagewa.
Ahmad Ali Ilu kurfi ya shiga makarantar a shekarar 2021, amma har ya ciri tuta a shekarar 2023.
Duk yaran da suka ciri tuta, an basu kyaututtukan karfafa gwaiwa.
Katsina city news
@ Www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779 .08057209539