Bikin Auren Jarumar Kannywood Ruƙayya Dawayya Da Shugaban Hukumar Tace Finafinai, Afakallah Ya Matso

..Samun Afakallah A Matsayin Miji, Allah Ne Ya Amsa Addu’a Ta – Dawayya
DAGA MUKHTAR YAKUBU
A YANZU da damina ta fara zuwa ƙarshe, hankalin wasu ‘yan fim ya koma kan batun auren nan da aka jima ana tsimayen sa, wato na jarumar Kannywood, Hajiya Ruƙayya Umar Santa (Dawayya) da Shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Alhaji Isma’il Na’abba (Afakallah).
Wasu da Majiyar Focus News Hausa, mujallar Fim ta zanta da su, amma su ka buƙaci a sakaya sunan su, sun ce sun ƙosa a zo a yi bikin, su na faɗin, “A gaskiya sun dace”.
Mujallar Fim ta ji daga wata majiya mai ƙarfi kan lamarin cewa shirye-shiryen bikin sun kankama.
A kan gaskiyar batun auren, majiyar ta ce: “To ai ba tun yanzu aka fara yin batun auren ba. Ko makaho a Kannuwood ya san akwai soyayya tsakanin Dawayya da Afakallah.
“Soyayya ce da aka daɗe ana yin ta a ƙarƙashin ƙasa, ba tare da sun bayyana wa duniya ta sani ba, sai a yanzu da aski ya zo gaban goshi ne ya sa ita Ruƙayya Dawayya ta fara ɗora hoton Afakallah a ‘status’ ɗin ta na WhatsApp da TikTok da kuma Instagram tare da yin wasu bayanai masu nuna alamar akwai soyayya mai ƙarfin gaske a tsakanin su.”
Majiyar ta ƙara da cewa: “Akwai maganar auren, kuma daga yanzu zuwa kowane lokaci za a iya yin sa.
“Ana cewa ba wani taro za a yi ba, za dai a ɗaura aure ne kawai amarya ta tare, amma dai mu mun dage a kan lallai sai an yi dina. Dawayya ba ƙaramar jaruma ba ce, kuma shi oga kowa dai ya san matsayin sa da muƙamin sa a gwamnati da ma siyasa. Don haka, za mu yi biki sosai.
“Da zarar sun kammala shirin da su ke yi, za a ji sanarwar ɗaurin auren. Ba wani abu ba ne da za mu ɓoye.”
“My hubby”, wato “Miji na”: Hoton Ruƙayya Dawayya da Isma’il Afakallah wanda jarumar ta wallafa a TikTok da Instagram
Wakilin mu ya lura da yadda jarumar, wadda kuma furodusa ce, ta mayar da al’amuran ta na soshiyal midiya ga Afakallah, musamman wajen wallafa hotunan sa da bidiyon sa, har ma da na ‘ya’yan sa, a shafukan ta. Shi ɗin ma ya na kula ta a duk lokacin da ta wallafa abin da ya shafe shi.
A saƙon da ta wallafa a Instagram a ranar 15 ga Yuli, 2022, Dawayya ta ce samun Afakallah da ta yi a matsayin miji, Allah ne ya amsa addu’ar ta. Ta ce, “Samun masoyi na gaskiya a wannan zamanin da rashin gaskiya ya yi yawa sai ƙarfin addu’a. Alhamdu lillahi ya Rabbi lakal hamdu wash shukhur. Allah na gode maka da ka amsa addu’a ta. Khairun nas man yanfa’un nas.”
Hoton sa da ta ɗora a ranar 14 ga Agusta tare da alamomin ƙauna da kuma addu’ar “Khairun nas man yanfa’un nas” ya ƙara bayyanar da soyayyar tasu a fili.
Ɗimbin ‘yan fim da sauran jama’a sun taya Dawayya da Afakallah murnar wannan abu da su ke shirin yi, su na faɗin Allah ya kai mu lokacin lafiya.
To, amin.