Zaharaddeen Mziag @Katsina City News
Tsohon Sakataren Gwamnatin jihar Katsina kuma shugaban yakin neman Zaɓen Atiku da Lado karkashin Jam’iyyar PDP Dakta Mustapha Moh’d Inuwa ya bayya, yanda tsohon Sanatan Yankin Funtua, Sanata Abu Ibrahim ya goyi bayan Dantakarar Gwamnan Katsina Satana Yakubu Lado Danmarke ta Karkashi kasa a shekarar 2011.
A taron da ya kira na Manema Labarai bayan kammala yakin neman Zaɓen yankin Daura wato (Daura Zone)
Dakta Inuwa ya bayyana godiya ga Dimbin Al’umma Masoya da magoya bayan jam’iyyar PDP inda suka fito kwai da Kwarkwata suka nuna soyayyarsu ga Jam’iyyar PDP da Sanata Yakubu Lado Danmarke, yace “Mungode kuma munawa Al’umma bangajiya.” Yace “Munga Masoya bama a Filin taro ba a bisa hanya cikin kauyuka ana fitowa ana mana fatan Alkhairi wannan ya nuna angaji da APC kuma am fahimci manufofin PDP, muna godiya.”
Da yake Amsa tambaya akan Maganganun da akace Dantakarar APC yayi akansa na zama Yaron Dantakararta, Inuwa ya bayyana cewa idan shi yaron Dantakara ne, ai shima Dangiwa yaron Dantakara ne, yace “Kara ma ni ace Lado da Atiku, shi kuma Radda ne kawai, ni nace Lado yaci arzikin Atiku.” Yace amma yasani Abu Ibrahim shine Ya fara goyawa Lado baya ta karkashin kasa a shekarar 2011 saboda yana kwadan a barmasa takararsa ta Sanata.” Yace Abu Ibrahim a boye ya goyi baya amma baisani ba duk abinda suke tataunawa da Lado yana zuwa ya fadimana.” Yace da muka hadu nake gayamasa sai ya nemi ya musanta maganar saida na kira Lado na sanya Speaker bayyane, Lado yayi magana yasan cewa dagaske ne, anan ido ya rainafata.”
Dakta Mustapha Inuwa yace “idan zamu fadi Magana muna kama suna so nake mutum yazo ya karyata yace ba’aiba.”
Dakta yayi bayani sosai game a sha’anin tsaro da kuma tanda za’a iya maganinsa inda ya Aika laifin kacokam a Gwamnatin Tarayya.