Zarah A Zamsarf
__ Dake nake ‘yar uwa mai karatu, ki sani abinda duk bakiyi a gida ba, baki koya kika saba dashi ba, to karki yaudari kanki cewan zaki yi idan kinyi aure, ko kice da kinyi aure zaki sauya ki fara yin yanda ya kamata.
__ Ina magana da ‘yammatan da wanka da wanki bai dame su ba, tsaftar jiki, gida data girki bata damesu ba, idan kayi musu magana sai kaji sunce, wai idan sunyi aure zasu gyara ai. To bari kiji, abinda kika saba kina yinsa tun a gida ma yana iya baki kunya a gidan aure, balle dama bayi kikeyi ba, kwatsam rana daya kike so ki wayi gari kiga kin saba da wannan abun. Anya munyiwa kanmu adalci kuwa ?
__ Akwai abubuwan da kike bukatar ki kware ba iyawa kadai ba, A’a ki kware ki goge ki saba dasu tun a gida, dansu ba a koyarsu lokaci guda, idan kuwa kinki ayi abin kunya. Misali :
Iya girki
Tsafta yayin girki
Tsafta ta gida data jiki ( wanke bandaki kullum bayan kin gama wanka, aske gabanki da hamatarki daidai lokacin da addini ya tanada dss)
Iya magana
Iya kula da miji
Iya kula da yara…. Wasu zasu iya cewa taya mutum zai iya kula da yaro bayan shi bai haifa ba, ana koya mana, bakida kanne, babu yaran yan uwanku, baki ganin yanda ake yiwa yaro ne, zaki iya koya idan kinso, saidai shi wannan akwai abubuwan da dole sai kin haifi naki sannan ki kware akai.
__. Wa’yancan dama wasu abubuwan da nasan ba saina fada ba har kin kawo su a ranki, kin kuma sansu dama can, suna bukatar jajircewarki ne tun a gida. Ba dare daya kina barin gidanku zakiga kawai duk kin iyasu, sun zame miki jiki ba.
Kuma ki sa wannan a ranki, su irin wa’yannan abubuwan koda kin iyasu kin kware idan basu bi jikinki ba suka zame miki dabi’a to da wahala ki dore koda kin fara, kuma kokarin su zame miki dabi’a din tun a gida zaki fara hakan, sai mafarkinki na bayan aure yazo miki da sauki.
__ Allah yasa kin fahinci inda nake son kaiki ‘yar uwa , ina sonki saboda Allah, ina fata mu hadu mu gyara duniyarmu da lahirar mu Allah yayi miki albarka 🤲🏼🌹
✍🏼