Za’a kammala aikin Gadoji da akeyi cikin Garin Katsina a watan Disamba na wannan shekarar Insha Allah, inji Yan’ Kwangila dake aikin Gadojin.

Yan’ kwangilar sun fadi haka ne yau lokacin da Alhaji Al-Amin Isah Darakta -Janar, Sabbin Kafafen Sadarwa na Zamani na Gwamnan Jihar Katsina ya jagoranci Kungiyoyin Coalition of Katsina State Media Support Groups zuwa duba ayyukan Gadar Sama da Kasa da Gwamnatin Jihar Katsina takeyi karkashin jagorancin Maigirma Gwamnan Jihar Katsina, Rt. Hon. Aminu Bello Masari. Gadojin da ake ginawa a Unguwannin Kofar Kaura, Kofar Kwaya, da kuma GRA duk a cikin Birnin Katsina.
Yan’ kwangilar sun tabbatar da cewa aikinsu yana tafiya yanda yakamata ba tare da wata matsala ba, wannan ne yasa suke bada tabbacin zasu kammala aikin a cikin watan Disamba na wannan shekarar kamar yadda suka yi alkawari lokacin da zasu fara aikin.
Wakilan ma’aikatar Ayyuka, Sufuri da Gidaje wadanda suka zagaya da Darakta-Janar din tareda tawagarshi sun kara tabbatar da cewa aikin zai kammalu cikin lokacin kamar yadda yan’ kwangilar suka fada.
Daga nan tawagar taje Kofar Guga inda suka duba sabuwar hanyar da Gwamnatin Masari tayi, hanyar wadda ta taso daga Bakin Kofar Guga ta shigo Sullubawa zuwa Masanawa yanzu haka an gama aikin nata wanda aka fara cikin watanni Shidda da suka wuce. Jama’ar da aikin yashafi Gidajen nasu a cikin Unguwannin sun tabbatar da tuni an biya su diyyar gidajen da aikin yashafa.
Wasu daga cikin mazauna unguwannin sun nuna jin dadin su da gamsuwar su akan aikin, tare da mika sakon godiyar su ga Maigirma Gwamna abisa aikin da akai masu, sun kuma shaida cewar bayan biyan diyya mai tsoka an kuma basu filaye domin su sake gina gidajen su. Daya daga cikin mutanen ya shaidawa Darakta-Janar da tawagarsa cewar wannan aikin hanya da akai masu su riba ma suka ci ta kowacce fuska aka kalli aikin, saboda haka suna godiya ga Maigirma Gwamnan Jihar Katsina Rt. Hon. Aminu Bello Masari.
Daga Ofishin Darakta-Janar, Sabbin Kafofin Sadarwa na Zamani Na Maigirma Gwamna.
24/10/2022.