Hukumar kiyaye haddura ta kasa, FRSC, ta ce ta samu jimillar hadurran kan tituna 19,787, RTCs, da kuma mutuwar mutane 9,227 a 2021 da 2022.
Shugaban riko na hukumar FRSC, Dauda Biu ne ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai a yau Litinin a Abuja.
Biu ya ce wani bincike na RTCs da hukumar ta gudanar ya nuna cewa tsakanin 2021 zuwa 2022, daga watan Janairu zuwa Disamba 2021, ta samu hadarurruka 10,304 a duk fadin kasar.
Ta ce RTCs 9,483 aka rubuta a daidai wannan lokacin a shekarar 2022, inda ya kara da cewa an samu raguwar kashi takwas cikin dari na hadarurrukan hanyoyin.
“Daga cikin hadurran da aka samu, hukumar ta yi nasarar rage yawan mace-macen kamar yadda kuma muka samu kashi takwas cikin dari na adadin mutanen da suka mutu.
“Misali, bayananmu sun nuna cewa a tsakanin watan Janairu zuwa Disamba 2021, mutane 4,800 sun mutu, yayin da a daya bangaren kuma, mutane 4,427 su ka rasu 2022,” in ji shi.