…….PDP ce ta lashe zaɓen Ɗan majalisar tarayya a shiyyar Batsari/Safana/Ɗanmusa.
A ranar asabar 25-02-2023 aka gudanar da babban zaɓe a faɗin tarayyar Najeriya.
A ƙaramar hukumar Batsari ta jihar Katsina, an gudanar da zaɓen cikin lumana ba tare da samu wata hatsaniya mai yawa ba, saɓanin lokutan baya inda akan yi kare jini biri jini yayin gudanar da zaɓukan, sai dai an samu jinkirin isowa da kayan zaɓe a dukkan mazaɓun dake faɗin ƙaramar hukumar, domin baa fara zaɓukan ba sai bayan ƙarfe ɗaya na rana wanda wannan jinkirin ya harzuƙa mutane da dama har ta kai wasu na zargin ana shirya maƙarƙashiya ga ɗan takarar Ɗan majalisar tarayya na babbar jam’iyyar hamayya ta PDP wanda ya fito daga ƙaramar hukumar Batsari, domin a sauran ƙananan hukumomin na Ɗan musa da Safana an fara zaɓen cikin lokaci.
Alhaji Ali Iliyasu Abubakar Ɗan-Alhaji na jam’iyyar PDP shine ya kara da Abdulƙadir Zakka na jam’iyyar APC wanda ya fito daga ƙaramar hukumar Safana, inda Ali Iliya ya kada Abdulƙadir Zakka da ratar ƙuri’u ƙasa ga dubu biyu. Koda yake an samu hatsaniya a zauren tattara sakamakon zaɓe dake Safana inda ake zargin shugaban ƙaramar hukumar Safana Kabir Umar yayi yunƙurin kutsawa cikin zauren da nufin kawo hargitsi, amma matasa suka dirar masa wanda saida jami’an tsaro suka harba barkonon tsohuwa, domin kawo daidaito. Daga ƙarshe dai an bayyana sakamakon zaɓen kamar yadda muka faɗa jam’iyyar PDP ce ta lashe zaɓen a shiyyar ta Batsari/Safana /Ɗanmusa. Wannan shine karon farko da ɗan ƙaramar hukumar Batsari ya samu damar zama ɗan majalisar tarayya tun dawo da mulkin farar hula a shekarar 1999.