Gwamna Aminu Bello Masari ya bayyana cewa wajibin mu ne, mu samar ma kawunan mu mafita daga dukkan matsalolin da muke ciki domin mun fi kowa sanin halayyar junan mu da kuma yanayin zamantakewar da muke da makwabtan mu da kuma na kasar kanta.
Gwamnan ya fadi hakan ne a yayin da ya amshi wani rahoto a kan hanyoyin shawo kan matsalar tsaro daga hannun shugaban gamayyar kungiyoyin Arewacin Najeriya Kwamared Jamilu Charanchi.
Ya kuma bayyana cewa makasudin kafa ko wace gwamnati shi ne kare rayuka da dukiyoyin al’umma, saboda haka wajibi ne a cire siyasa a cikin lamarin tsaro a nemi hadin kai da gudummuwar kowa domin tabbatar da an cimma burin kafa gwamnatin.
Alhaji Aminu Bello Masari ya kara da cewa, a wannan iskar mai kadawa, ana bukatar Matasa su zamo masu fikira, tunani da sanin ciwon kai, ta yadda za su iya zama su bada gudummuwar su ta yin nazari a kan duk halin da aka sami kai; idan mai dadi ne sai a samar da yadda za aci ribar shi, idan kuma marar dadi ne sai a nemi yadda za a sami mafita, domin a gudu tare a tsira tare.
Ya kuma shawarci Matasa da su rika neman hanyoyin tattaunawa da shuwagabanni a duk lokacin da wata mas’ala ta taso, ba hanyar fito-na-fito ba, da a yanzu mafi yawan Matasa suke yi tare da zugar ‘yan siyasa.
Gwamnan ya kuma yi kira ga wannan gamayyar kungiyoyi da su fadada ayyukan su na nazari, domin su hada koyar da sana’o’i tare da samar da ayyukan yi ga Matasa. Yin hakan zai rage raɗaɗin zaman takaici da matasan suke yi a majalisu da sauran wuraren da suke zaman jiran gawon shanu.
Tun farko a nashi jawabin, Kwamared Jamilu Charanchi, ya bayyana cewa Gwamna Aminu Bello Masari ne na farko da ya basu lokaci suka gabatar mashi da kudurorin su na kafa wannan gamayya ta kungiyoyin arewa tare kuma da basu damar bada tasu gudummawa a rubuce a kan hanyoyin da za abi domin shawo kan matsalar tsaro da ta addabi arewacin kasar nan.
Kwamared Charanchi ya kara da cewa wannan rahoto da suka gabatar wa Gwamna Masari, ya kunshi hanyoyin da suke ganin bin su zai kawo karshen wannan matsala ta tsaro. Ya ce sun mika wa Gwamnan rahoton a matsayin shi shugaban kwamitin tsaro na kungiyar Gwamnonin jihohin Arewa, tare da fatar isar da wannan rahoto ga duk Gwamnonin jihohin domin yin nazari da kuma aiwatarwa.
