Ofishin Majalisar Dinkin Duniya mai kula da yammacin Afirka da Sahel, UNOWAS, na hada kai da ƴan takarar shugaban kasa da sauran masu ruwa da tsaki a Nijeriya domin tabbatar da zaben kasar cikin lumana.
Giovanie Biha, mataimakiyar wakilini na musamman na babban sakataren MDD kuma jami’in kula da harkokin hukumar ta UNOWAS, ta bayyana hakan a jiya Talata a birnin New York yayin da ta ke gabatar da sabon rahoton UNOWAS ɗin da ya kunshi abubuwan da suka faru cikin watanni shida da su ka gabata.
Biha ta ce ofishin ya kuma shaida rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a tsakanin jam’iyyun siyasa a Najeriya domin inganta zabe cikin lumana.
“A jihar Kaduna, a watan Disamba 2022, Ofishin Jakadancin ya goyi bayan taron farko na masu ruwa da tsaki a matakin Jiha shida don inganta zabe cikin lumana. A jamhuriyar Benin, an gudanar da zaben ƴan majalisar dokokin kasar cikin kwanciyar hankali kwanaki biyu kacal da suka gabata,” inji ta.
A cewarta, ko da yake yammacin Afirka da yankin Sahel na ci gaba da fuskantar kalubalen tsaro da ba a taɓa ganin irinsa ba, amma har yanzu “kasa ce mai dimbin damammaki”.
Jami’iar ta Majalisar Dinkin Duniya, ya bukaci jakadun da su ci gaba da ba da goyon baya ga dabarun da suka shafi karfafa juriya, inganta shugabanci nagari, da karfafa zaman lafiya da tsaro.