• About us
  • Advertise
  • Privacy Policy
  • Contact
Monday, January 30, 2023
  • Login
Katsina City News
Advertisement
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta
No Result
View All Result
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta
No Result
View All Result
Katsina City News
No Result
View All Result
Home Sashen Hausa

Ɗan takarar gwamna na NNPP a Kano ya maka shugaban APC na jiha s kotu bisa kalaman tunziri

January 6, 2023
in Sashen Hausa
0
Ɗan takarar gwamna na NNPP a Kano ya maka shugaban APC na jiha s kotu bisa kalaman tunziri
0
SHARES
20
VIEWS
Share on FacebookShare on Twitter

Ɗan takarar gwamna na jam’iyyar adawa ta New Nigeria Peoples Party, NNPP, Abba Yusuf, ya maka shugaban jam’iyyar APC mai mulki na Kano, Abdullahi Abbas, a kotu, bisa zarginsa da kalaman tunziri da na ɓatanci.

Yusuf, a karar mai lamba FHC/KN/CS/02/2023 da lauyansa Bashir Tudunwuzirchi ya shigar, ya bukaci babbar kotun da ta gaggauta tilasta wa kwamishinan ƴan sandan jihar Kano da ya binciki shugaban jam’iyyar APC tare da gurfanar da shi a gaban kuliya a bisa “kalaman da ke haifar da tashin hankali na siyasa a jihar”.

Sanarwar mai dauke da sa hannun mai magana da yawun dan takarar, Sanusi DawakinTofa, ta ce dan takarar gwamnan NNPP ya garzaya kotu da nufin tunatar da ‘yan sanda su yi abin da ya kamata.

“Mun rubuta korafe-korafe da dama tare da ƙwararan hujjoji kan yawan ta’asar da shugaban jam’iyyar APC na jihar ya yi, amma har yau hukumar ƴan sanda a Kano ba ta yi wani aiki a kan su ba.

“A ƴan kwanakin nan, Abdullahi Abbas, dansa Sani Abdullahi Abbas da wasu makusantansa ne suka shirya tashe-tashen hankula na siyasa da dama, inda aka raunata wasu da ba su ji ba ba su gani ba, aka raunata su da kuma tsoratar da su amma duk da haka, ‘yan sanda sun yi shiru a kan lamarin duk da rubutaccen korafin da aka gabatar musu. ,” in ji sanarwar.

Idan har kotu ta amince da umarnin, za ta tilastawa rundunar ‘yan sandan Kano sauke nauyin da kundin tsarin mulkin kasar ya dora mata, tare da yin aiki da irin wannan korafin da aka rubuta a kan shugaban jam’iyyar APC na jihar, Abdullahi Abbas kan zargin kalaman nuna kiyayya, cin zarafi da kuma tallata ‘yan bangar siyasa.

Share

Related

Source: Daily Nigeria
Via: Katsina City News
Previous Post

Police Repel Terrorists Attack, Kill One, Rescue Victim In Katsina

Next Post

History of katsina Districts (II) By Prof Sani Abubakar Lugga

Next Post
History of katsina Districts (II) By Prof Sani Abubakar Lugga

History of katsina Districts (II) By Prof Sani Abubakar Lugga

Recent Posts

  • APC ta gano kafafen yada labaran da PDP ke ɗaukar nauyi su yaɗa karya a kan Tinubu
  • Emefiele: We’ve collected N1.9trn old naira notes so far — N900bn more to go
  • Hanyoyi Shida Domin Kiyaye Basir Cikin Sauƙi.
  • Bankin CBN Ya Samar Da Naira Miliyan 120 Domin Yin Canjin Kudi A Katsina.
  • INEC ta kara tsawaita wa’adin karbar katin zabe

Recent Comments

No comments to show.

Archives

  • January 2023
  • December 2022
  • November 2022
  • October 2022
  • September 2022
  • August 2022
  • July 2022

Categories

  • Biography
  • City News
  • Condolence
  • Fasahar zamani
  • Featured
  • General Stories
  • History
  • Kula da Lafiya
  • Labaran Fim
  • Literature
  • News and Analysis
  • News and Reports
  • Photo News
  • Rubutu da Marubuta
  • Sashen Hausa
  • Tarihin Kasar Katsina

Browse by Category

  • Biography
  • City News
  • Condolence
  • Fasahar zamani
  • Featured
  • General Stories
  • History
  • Kula da Lafiya
  • Labaran Fim
  • Literature
  • News and Analysis
  • News and Reports
  • Photo News
  • Rubutu da Marubuta
  • Sashen Hausa
  • Tarihin Kasar Katsina
  • About us
  • Advertise
  • Privacy Policy
  • Contact

No Result
View All Result
  • Home
  • News and Analysis
  • Biography
  • History
  • Photo News
  • Featured
  • Literature
  • Sashen Hausa
  • Weekly Columns
    • Allo
    • Fasahar Zamani
    • Kula da Lafiya
    • Labarun Fim
    • Rubutu da Marubuta

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In