
Ana zargin jami’an Ƴansanda da buɗe wuta ga Masu kiɗin DJ da yayi sanadin Mutuwar yara biyu a Unguwar Tudun Matawalle cikin Birnin Katsina
Da Yammacin ranar Lahadi a Unguwar Tudun Matawalle dake cikin Birnin Katsina jami’an ‘Yansanda sun farwa masu shagalin biki da yayi sanadiyar rasa wasu yara ‘yan ƙasa ga shekaru goma a wajen Kiɗan.
Kamar yanda ɗaya daga cikin Iyayen yaran da abin ya shafa ya bayyanawa Jaridar Katsina City News, “Jami’an na ‘Yansanda sun shiga Unguwar inda suka iske ana kiɗan DJ don gudanar da Biki, bisa Al’ada cewa a garin Katsina idan ana wata sabga akan ɗauko masu kiɗan DJ don murna da shagalin bikin.” Yace ‘Yansandan sun shiga Unguwar suka cewa Matasan da ke kidan da su tashi subar wajen, amma sukaƙi su tashi, sakamakon haka ne ‘Yansandan suka buɗe wuta kan mai uwa dawabi, inda lamarin ya rutsa da wasu yara da suka taso daga Islamiyya zuwa gida.”
Majiyar ta shedawa Jaridunmu cewa Yara biyu da suka mutu sakamakon harbin harsashi, basu gaza shekaru goma ba, inda mutum uku suka jikkata suna Asibiti.
Malam Musa Ali, malami ne na makarantar Islamiyya da ya rasa ɗalibinsa guda ɗaya ya bayyanama Jaridun mu cewa, “Ɗalibin namu mai shekaru tara yazo makarantar yamma harma ambiya masa Allonsa ya wanke ammasa wani sabon rubutu, bayan an tashi akan hanyarsa ta zuwa gida, abin ya rutsa da shi, bamu ma san halin da ake ciki ba, sai washe gari mahaifiyar yaron tazo makarantar take cewa aikuwa yaronnan ga abinda ya sameshi har ma Allah yayi masa rasuwa.”
Mun aika sako don jin ta bakin hukumar ƴansanda, zuwa haɗa wannan rahoto bamu samu amsa ba.