A daren Ranar Asabar 21-01-2023 da misalin ƙarfe 03:00am na dare ɓarayin daji suka sake kawo harin ta’addanci a unguwar Dutsinma wacce wasu ke kira unguwar mata zalla dake cikin garin Batsari hedikwatar ƙaramar hukumar Batsari ta jihar Katsina. Sun afka gidan wani bawan Allah mai suna Mallam Hamisu Ɗan kes, inda suka fafata da shi har sukaci ƙarfin shi, domin da shigar su cikin ɗakin shi, sai ya rungumi mai mutum ɗaya dake da bindiga a cikinsu, wannan yasa wasu daga cikinsu suka kama saran shi da adda kamar ana saran kabushi. Sunyi masa munanan sara a kai da ƙafa(agara), hannuwa da cikin shi, suka bar shi cikin jini kwance, sannan suka sace dabbobi da babur ɗin shi. Yanzu haka yana babbar asibitin Batsari cikin mawuyacin hali, koda yake yana samun kyakkyawar kulawar likitoci. Sunyi ƙoƙarn ɓalle wasu gidaje amma dai basu samu saa ba, wannan ya sabbaba tare da jefa mutanen unguwar shiga mawuyacin halin rashin tabbas, ganin cewa ko mako ɗaya baa kulle ba ɓarayin suka shigo suka kashe wani mutum kuma suka sace masa shanu ukku.