
Hukumar Gudanarwar Jami’ar Abuja Ta Amince Da Naɗa Barista Aisha Maikuɗi, Yar Asalin Jihar Katsina, Wadda Ita Ce Farfesa Mafi Ƙarancin Shekaru A Matsayin Mataimakiyar Shugabar Jami’ar Abuja, Mai Kula Da Mulki, Yau Litinin.
Bayanin Hakan Na Kunshe A Cikin Wata Takardar Da Jami’ar Ta Fitar Yau Litinin, Inda Ta Ce Biyo Bayan Zama Hukumar Gudanarwar Jami’ar Karo Na 96 Da Aka Gudanar A Ranar Alhamis Da Juma’a, 4 Zuwa 5 Na Watan Mayu, 2023 Ta Amince Da Naɗa Farfesa AishaWanda Ya Fara Aiki Daga Ranar 5 Ga Watan Mayu Na Tsawon Shekara Biyar Masu Zuwa. Farfesa Aisha Maikuɗi, Wadda Ke Da Kwarewa Kan Dokokin Ƙasa Da Ƙasa, Tana Da Shekara 40 A Duniya Kuma Ta Zama Farfesa A Shekarar 2022.
Allah Ya Taya Riko!