Da safiyar yau Litinin 26/09/2022 Ɓarayin daji ɗauke da muggan makamai suka kai harin ƙwanton Ɓauna ga Jami’an tsaro dake ƙauyen ƙwarare, Makera akan hanyar Jibia zuwa Katsina Inda suka halaka wani Jami’in tsaro Inspector Idris Musa tare da ƙona motar shi.
Bayanai da suke fitowa daga yankin sunce Ɓarayin sun raunata wasu Mutanen da ba’a tantance wa ba tare da kora wasu Mutane suma da ba’a San adadin su ba zuwa Daji.
Har kawo yanzu dai babu takamaimai ƙarin bayani akan wannan Ibtila’in da ya afku a safiyar Yau ɗin nan.
Source:
JMC
Via:
Katsina City News