Da hantsin yau Lahadi ne ƴan uwa almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky suka gudanar da aikin tsaftace babbar Asibiti da ke cikin garin Ɓatagarawa jihar Katsina.
Ƴan shi’an sun haɗu ne tare da ƴan Si-Caunt a ya yin da suka gudanar da aikin. Aikin wanda ya haɗa da nome ciyawar da ta mamaye Asibitin, da kuma tsaftace ɗakunan majinyata.
Bayan kammala aikin, Malam Nafi’u Hassan ya ya gabatar da IC na Babbar Asibitin, inda ya yi godiya ga ƴan uwa da kuma ƴan Si-Caunt akan wannan babban aikin da suka yi na tsaftace Asibiti. Daga karshe an yi Addu’a Kuma aka sallami kowa.
Rahoto: Usman Umar Katsina.
Hoto: Ishaq Abdullahi
Source:
Katsina City News
Via:
Zaharadeen Mziag