Rundunar ƴan sandan jihar Zamfara ta ce wasu ƴan gida bakwai ne suka mutu bayan sun ci dambu domin cin abincin dare.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, SP Mohammed Shehu, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na ƙasa cewa rundunar ta fara gudanar da bincike domin gano musabbabin mutuwar ƴan gida dayan, mazauna Danbaza da ke Ƙaramar Hukumar Maradun ta jihar.
“Al’amarin ya faru ne a ranar Litinin bayan da ‘yan gida ɗaya suka ci abincin a matsayin abincin dare.
“‘Yan sanda sun dauki samfurin abincin don yin gwaji kuma ina tabbatar wa jama’a cewa za a fitar da sakamakon ga manema labarai,” in ji Shehu.
Wani mazaunin kauyen, Muhammad Kabir, wanda na kusa da iyalan ne, ya shaida wa NAN cewa huɗu daga cikin wadanda lamarin ya rutsa da su da suka haɗa da matan aure biyu da matasa biyu sun mutu nan take yayin da sauran ukun suka mutu bayan an garzaya da su asibiti.
” gama cin abincin masu ke da wuya, sai huɗu daga cikinsu suka mutu nan take.
“An garzaya da sauran ukun asibiti, amma daga baya sun mutu a lokacin da suke karɓar magani,” in ji Kabir.