Misbahu Ahmad Batsari
@Katsina City News
Da sanyin safiyar yau juma’a 02/12/2022 wasu gungun ƴan bindiga da ake tsammanin sun kai babur 25 suka dira garin Ƙarare dake cikin yankin ƙaramar hukumar Batsari ta jihar Katsina, inda suka yi tara-tara suka kora mutane aƙalla 40 daji.
sun kuma bindige wani bawan Allah da ake kira Malam wanda shine yake kula da asibitin garin a matsayin atenda.
Ganau sun tabbatar mana da cewa ƴan bindigai sun shigo garin ne dai-dai lokacin da mutanen garin ke kalaci kafin su shiga harkokin su na yau da kullum.
A wani labari kuma wasu ƴan bindiga sun kashe mutane biyu a ƙauyen Sabon garin gamji dake yankin ƙaramar hukumar Safana yau jumma a da misalin ƙarfe 2:30pm na rana. Shi wannan ƙauyen ya gab da garin Wagini ta Batsari.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com