Misbahu Ahmad Batsari
@ katsina city news
Da misalin ƙarfe ukku 3:00am na daren jiya litanain 10-01-2023 ɓarayin daji masu satar dabbobi, garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa, suka kai hari cikin garin Batsari hedikwatar ƙaramar hukumar Batsari ta jihar Katsina.
Ɓarayin sun taka katanga suka faɗa gidan wani bawan Allah mai suna Malam Abdulmalik dake zaune a unguwar Dutsinma inda suka ɓalle ƙyauren gidan sannan suka ɓalle ɗakin matarsa suka yi awon gaba da ita da babur ɗin shi. Sannan sun shiga gidaje huɗu bayan nashi, inda suka karɓe wayoyin magidantan kuma suka kore masu tumaki da awaki.
Wani da abun ya rutsa da shi ya bayyana mana cewa sun iske shi ɗakin matar shi suka ƙwace wayar shi sannan suka sabke mashi kwando zagi kuma sukace idan ya sake ya fito sai sun kashe shi.
Mafi yawancin mazauna unguwar sun bayyana mana cewa sun nemi taimako tare da yin kururuwar neman taimako,amma duk a banza, haka suka kora dabbobin, suka tura babur ɗin a ƙasa ba tare da samun wata tangarɗa ba.
Sai dai da yawan waɗanda suka yi ido huɗu da ɓarayin sun bayyana cewa akwai hausawa a cikin su.
Ita wannan unguwa ta Dutsinma tayi ƙauran suna wajen hare haren ƴan bindiga cikin ƴan kawanakin nan domin cikin makkonni ukku ɓarayin sun shigo unguwar ba adadi kuma har kisan kai sunyi sun sace dukiya mai yarin yawa amma har yanzu ba wani matakin daƙile hare haren da aka ɗauka.
Har rubuta rahoton nan babu wata sanarwa daga jami an tsaro akan farmakin
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com
07043777779 08137777245