Misbahu Ahmad batsari
@ katsina City News
Da misalin ƙarfe 2:00am na daren jiya talata 28-12-2022, ƴan bindiga masu satar dabbobi da garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa suka kai hari cikin garin Batsari ta jihar Katsina, ƴan bindigar sun afka unguwar dutsinma inda suka faɗa gidan wani Malam Tasi’u mai sana’ar saida ganda inda suka bindige shi kuma suka kore dabbobin shi. Majiyarmu tace baa samu wani ɗauki daga maaikata ba.
Dama ko a makon da ya gabata ƴan bindigar sun kawo hari unguwar ta dutsinma inda suka sace awaki da tumaki aƙalla guda goma sha biyar.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com