….sun ƙone motoci biyu ƙurmus, kuma sun jikkata mutum huɗu.
Misbahu Ahmad batsari
@ katsina city news
A ranar alhamis 12-01-2023 da rana tsaka wasu ƴan bindiga dake kan babura suka tare motocin ƴan kasuwa da suka fito daga ƙauyen Ƴanɗaka zuwa kasuwar Batsari inda suka buɗe wuta ga motar wani mutum mai suna Abu dogon direba.
Maharan sun suka jikkata mutum huɗu ciki hadda wata dattijuwa wacce suka yima mummunan harbi a fuska.
An garzaya da matar asibitin Katsina, domin ceto rayuwar ta, sauran mutane ukku kuwa suna asibitin Batsari ana yi masu magani.
Bayan wannan mummunan aiki da suka yi a daidai kwalbatin dake kan hanyar furaja daga Ƴandaka zuwa Tashar-Nagulle sai kuma suka kutsa cikin garin na Ƴanɗaka inda suka iske ana lodi a tasha, nan take suka cinnama motoci biyu wuta ɗaya ma tana ɗauke da buhunnan auduga da za a kai kasuwa. Motocin da suka ƙone akwai motar wani mai suna Muhammadu Chalo ƙirar golf da ta wani mai suna Ɗan Ade Bado itama ƙirar golf.
Har rubuta labarin nan babu wata maganar da Rundunar yan sanda akan wadannan hare hare guda biyu.
Katsina city news
@ www.katsinacitynews.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai.com
The links news
@ www.thelinksnews.com