A ranar Talata 29 ga watan Nuwamba Kungiyar yaƙin neman zaɓen Lado Danmarke mai suna “Ladon Alkhairi Movement” ta miƙa mubayi’arta ga sabon shugaban jam’iyyar PDP na riƙo Alhaji Lawal Magaji Ɗanɓaci, da Daraktan yaƙin neman zaɓen Atiku da Lado a jihar Katsina Dakta Mustapha Muhammad Inuwa.
Da yake jawabi a taron sakataren kungiyar Ladon Alkhairi, Hon. Albaba ya bayyana Ayyukan kungiyar da yanda ta samu karbuwa ga mutanen jihar Katsina,
Shugaban kungiyar Ladon Alkhairi Dakta Musa Gafai ya bayya yanda sukayi tsari domin cin zaben 2023 sana ya tabbatar wa shugaban jam’iyyar PDP cewa suna da ofisoshin Ladon Alkhairi a ko ina fadin jihar Katsina, tare da ma’aikata jajirtacci da zasu tsaya kai da fata don ganin PDP ta samu nasara tun daga sama har kasa. Sana kuma Musa Gafai ya gabatar da takardun Ayyukansu ga Shugaban jam’iyyar da Bana ta Ofis mai dauke da suna da Hoton Shugaban jam’iyyar.
Da yake jawabi a madadin jam’iyyar tasu ta PDP Hon. Lawal Magaji Danbaci ya bayyana jin dadinsa ga kungiyar da jagororin ta, bisa ga irin yanda Suke gudanar da Aikace-aikacensu. Yace shima Danƙungiyar Ladon Alkhairi ne, don haka idan aka kafa Gwamnati dole suje suji mi Gwamnati zataiwa Ladon Alkhairi?
Danbaci yayi kira ga ‘ya’yan jam’iyyar ta PDP da suyi hakuri suzo a hada kai ayiwa jam’iyya aiki, yace nasara bata tabbata saida kalubale, yace wannan halin da ake ciki shine kalubalen, kuma ya yi nasiha da bada misalai cewa babu wanda ke samun Nasara dari bisa dari kuma tarihi ne tun lokacin Annabawa da sahabbai.
Daga nan kungiyar ta Ladon Alkhairi Movement ƙarƙashin jagorancin Musa Gafai suka isa Ofishin Dakta Mustapha Inuwa DG Kamfen na Lado/Atiku 2023 inda suka mika mubaya’a da tayashi murna ta zama Daraktan yakin neman Zaɓen Atiku da Lado. Mustapha Inuwa ya ji dadi sosai ga ziyarar inda ya bayyana Musa Gafai a matsayin wakilin shi, yace “Munsan idan akwai ire-iren Musa Gafai to munsan mun bar baya, sai mu tattara yanamu yanamu mu koma gefe, mubar masu jini a jika,” yace Musa Ga Karfi, ga Kayan Aiki, ga Iya aikin don haka lallai Musa Mai kwazo ne. Yace yanawa kira ga Kungiyar Ladon Alkhairi da ta shirya ranar 19 ga wata a fito da karfi ayiwa APC Bugun Kutufo ta suma, ranar Rantsuwa su zo su kwasheta suje suyi mata jana’iza. Yace ranar 19 ga wata shine ranar da Atiku zaizo Katsina don haka duk dan jam’iyyar PDP ya zama cikin shirin kawo karshen APC.