A ranar Lahadi 22 ga watan Janairu Kungiyar da ke fafutukar ganin Hon. Sani Aliyu Danlami (Mai raba Alkhairi) ya lashe zaben majalisar dokoki ta Tarayya a Mazabar Karamar Hukumar Katsina wato Danlamiyya Amana ƙarƙashin jagorancin Hon. Jamilu ‘Yan’alewa ta rabawa Malaman Makarantun Allo kayan Abinci da tabarmi domin ciyar da Almajiransu.
Da yake tsokaci a wajen taron bada Tallafin Hon. ‘Yan’Alewa ya bayyana cewa, “Acikin Al’umma Malamai ne musamman na Addini su sukafi bada gudunmawar Tarbiyya irin wadda Iyaye ke bawa ‘Ya’yansu.” Yace “bayan iyaye Malamai magada Annabawa sune ke daukar wannan nauyi na Tarbiyyar yara, kuma sun cancanta a gode kuma a jinjina masu.” Yace “Shiyasa wannan kungiyar ta Danlamiyya Amana tayi duba akan cewa itadai kam Malamai zata tallafawa da wadannan kayan masarufi don rage nauyin da ke kansu na ciyar da Almajirai da basu tarbiyya”.
Jamilu ya bayyana kokon bararsa ta Addu’a ga malamai akan Aniyar su ta zabe mai zuwa da kuma Dantakarar su na Jam’iyyar APC Hon Sani Aliyu Danlami.
An zabo wasu daga cikin malamai Makaranta Alqur’ani mai girma daga kowace Mazaba a karamar hukumar Katsina domin basu Tallafin Buhun Masara, Dawa, da Tabarmi.
Taron da aka gudanar a dakin taro na EEC akan hanyar Kano ya samu halartar Ciyaman na kungiyar Danlamiyya Amana, Hon.Jamilu Yan’alewa,
Ciyaman na jam’iyyar APC na katsina Alh. Shamsu Ummar, Kansiloli da super viseary Kansila sun halacci wannan taro,daga kowace mazaba.
Tun da farko angabar da Addu’a ta musamman ga ƙasa da Jihar Katsina domin samun dauwamammen zaman lafiya daga Alarammomi da suka halarci taron.