Kungiyar “Citizens Participation Agains Curraption Initiative” ta shirya zama na musamman da kungiyoyin Matasa don kaucewa Rikicin Zaɓe

Kungiyar ƙarƙashin jagorancin Dan Gwagwarmaya Comrade Bishir Dauda ta shirya taron a Sakatariyar Kungiyar ‘Yanjaridu ta ƙasa reshin jihar Katsina a ranar Asabar, inda ta gayyaci kungiyoyin Matasa, da masu ruwa da tsaki akan shirya zaɓe da wayar da kai, Irin su Hukumar gyara ɗabu’a ta ƙasa NOA, da Hukumar INEC, da Kungiyar ‘Yanjaridu ta ƙasa reshen jihar Katsina NUJ.
Da yake bayyana maƙasudin taron Comrade Bishir Dauda ya bayyana dalilin wannan haɗuwa da wakilan ƙungiyoyi daban-daban domin haɗuwa a tattauna yanda za’a iya wayar da kan al’umma domin kaucewa rikicin zaɓuka masu zuwa, da kaucewa shiga bangar Siyasa.

Comrade ya bayyana ire-iren Aikace-aikace da ƙungiyar take da kuma wanda zata tunkara a nan gaba, yace musamman sanya ido a kalaman ‘Yan Siyasa wanda zasu iya tada zaune tsaye, yace kungiyar a shirye take da ta binciki tare da kai ƙarar duk wani ɗan Siyasa da yake kalaman ɓatanci da zasu iya jawowa ƙasa rashin zama lafiya. Da yake jawabi a wajen taron tsohon Darakta a hukumar gyaran aƙida ta ƙasa NOA, Comrade Yusha’u Mani ya ja hankalin matasa akan kaucewa ɓarna da ɗora rayuwar su bisa turbar da ta dace, yace “Mu da kuke gani masu yawan shekaru zamu iya cewa tamu ta ƙare mun yi karatu kyauta, munyi aikin gwamnati kuma mun gama, ku yanzu kune zaku gina gobenku.” Yace abin bakinci shine, yau tsaffin da suka mori ƙasar nan suka samu ilimi da rayuwa mai inganci, sune yau suke jafa matasa cikin halin laha’ula,i.” Comrade Mani ya yi kira ga malamai da suji tsoron Allah, su daina hawa mimbari suna amfani da Addini domin yaɗa fitina cikin Siyasa, yace siyasa ba Addinin bace, adaina amfani da Addini wajen wawaitar da hankalin mutane a Siyasa.
Shima da yake tsokaci a wajen taron wakilin hukumar zaɓe ta INEC a jihar Katsina, PRO na hukumar ya bayyana kokarin da suke na ganin an yi zaɓe cikin kwanciyar hankali da tabbatar wa Al’umma cewa yanda suka shirya zaɓen bisa adalci, da tsari, babu batun maguɗi a cikinsa, yace shiyasa ma wasu ke tsoron Na’urar zaɓen saboda suna ganin ba zata yi masu abinda suke so ba. Sannan yasha alwashin cewa zaɓe ne na gaskiya kuma ko wanene yaci zaɓe za’a tabbatar masa da zaɓensa.
Da yake Magana shugaban NUJ na jihar Katsina da ya samu wakilcin Comrade Aminu Musa Bukar, ya bayyana Illolin rashin zama lafiya a cikin al’umma, yace “Mu ‘Yanjarida muke da rauwar da zamu taka wajen fadakar da mutane, illar hakan.” Yace idan babu zama lafiya ko nan wajen taron ma ba zamu iya zuwa ba, don haka zama lafiya shine farko kafin komai.
Shugabannin kungiyoyin farar hula daban-daban ne suka halarta kuma suka tofa albarkacin bakinsu, gami da kira ga wannan ƙungiya da kada ta gajiya taci gaba da irin wannan tarurruka domin wayar da kai.
Daga cikin bakin da suka halarci taron akwai Bashir Dauda, Aminu Musa Bukar, Comrade Salisu Hafijo, comrade Hamza Umar Saulawa, Comrade Muntari Lawal Tsagem, Comrade Nura Siniya ‘Yan jaridu da sauran kungiyoyin.