Daraktan yakin neman Zaɓen Atiku/Lado 2023, Dakta Mustapha Moh’d Inuwa Ya bayyana Adadin mutanen da suka fice daga jam’iyyar APC da wasu jam’iyyu zuwa jam’iyyar PDP da yakai Adadin dubu sha Bakwai da ɗari uku da saba’in da uku, yace Mutanensu ba na boge bane da wasu suke karya a busa takarda.
Shugaban jam’iyyar PDP na jihar Katsina Hon. Magaji Ɗanɓaci ya karbi dandazon mutanen daga jam’iyyar APC da wasu jam’iyyu da kungiyoyin da suka yarda zasu zabi PDP daga sama har kasa.
A Ranar Litanin 16 ga watan Janairu tawagar Dantakarar Gwamnan na jihar Katsina Sanata Yakubu Lado Danmarke ya sauka garin Bindawa don bayyana takarar sa ga Al’ummar Bindawa inda jama’a suka fito maza damata don tarbar Dantakarar, Sanata Yakubu Lado Danmarke a wajen jawabin nasa ya bayyana irin gagarumin cigaba da zai kawo idan Allah ya sanya Al’uma sun zaɓeshi a matsayin Gwamnan jihar Katsina, yace “Kowa yasan irin yanda a ka baro a baya yanda PDP ta tsare hakkokin jama’a Ilimi kyauta, Haihuwa kyauta, Takin Zamani mai Rahusa, Albashi akan Lokaci da duk wasu hakkoki.” Yace muna so mu maido da wannan tsari idan Allah yasa kun zabi PDP daga sama har ƙasa.