A cigaba da rabon kayayyakin Amfani ga Zawiyyoyi, Tsangayu da Masallatai da Kungiyar yaƙin neman zaben Bola Ahamed Tinubu da Dakta Dikko Umar Raɗɗa mai suna “Asiwaju Gwagware gida-gida” take a ranar Juma’a 23 ga watan 12 na shekarar 2022 wakilan kungiyar ƙarƙashin jagorancin Alh. Aliyu Ilu Barde ta shiga ƙaramar Hukumar Dutsin-ma da ƙaramar Hukumar Kurfi, inda suka raba kayayyakin Amfani ga yara, makaranta Alqur’ani da Zawiyyoyi, Tsangayu da kuma Masallatai.
Zawiyya da Tsangayu da suka amfana da Tallafin a garin Dutsin-ma da Kurfi sun haɗa da
1-Zawiyyar Bani Adam Hayin Gada Dutsen ma.
2-Hayin gada 2, Makarantar Malam Abdullahi Bature
3-Kanti, tsangayar Malam Hamza
4-Masallacin Tanki, Abba Jaye Road
5-Masallacin Ahalussuna na gidan Baba Jalli duk a garin Dutsin-ma, sai kuma garin Karofi a cikin Ƙaramar Hukumar ta Dutsin-ma.
6-Ƙaramar Hukumar Kurfi Unguwar Saulawa Zawiyyar Malam Lawal Liman.
Duka Zawiyyoyin ga wadanda suke da Makaranta Alqur’ani wato Tsangayun Allo sun amfana da Tabarmi, Barguna, Butoci, da Shadda da kudin Dinki, inda su kuma Masallatai suka amfana da Butoci da Tabarmi. Ƙungiyar ta bakin Shugaban nata Hon. Aliyu Ilu Barde sun bayyana cewa sun tanadi Bandir din Shadda dari biyar, Butocin Al’wala Dozin dari biyar, Barguna ɗari biyar, da Tabarmi ɗari biyar da zasu raba a dukkanin kananan hukumomi 34 na jihar Katsina. A farkon watan Disamba ne shugaban kungiyar ya jagoranci raba kayayyakin a Tsangayun ƙaramar Hukumar Katsina inda suma suka amfana da irin wannan Tallafin.