A jiya Litanin Shugaban ‘Yan shi’a a Najeriya ya karɓi baƙuncin ziyarar wasu ƙabilar Igbo daga wasu sassan yankuna daban daban na Najeriya, inda suka ziyarce shi da gaisheshi, gami da neman Shawarwari daga bakin jagoran ‘Yan shi’ar.
Bayan ziyarar ne, da tattaunawa wani daga cikin ƙabilar ta Igbo ya amshi musulunci inda ya zaɓi a sanya masa suna Muhammad Musa.
Wannan ziyarorin da jagoran ‘Yanshi’a ke karɓa ba sabon abu bane tun bayan fitowarsa daga gidan Kurkuku da ya kwashe tsawon shekaru kusan shida a tsare, bisa zargin taron tare hanya ba bisa ƙa’ida ba, wanda daga bisani Kotu ta wanke shi,’. a baya-bayannan Manyan ‘yan siyasa a Najeriya sun ziyarci Shehin Malamin, inda suka tattauna al’amura da dama.
Sheikh Ibrahim Zakzaky shine shugaban Mazhabin shi’a a Najeriya wanda ya fuskanci Muzgunawa mafi muni a tarihi inda aka kashe mashi ‘Ya’ya shida a lokutta daban-daban aka rusa gidansa da duk wata kadara da ya mallaka a garin Zariya, gami da kashe ɗaruruwan mabiyansa a shekarar 2015.