…Zai Amshi Sandar Mulki Gobe

…Yadda Aka Shirya Bikin Ba Shi Sandar

*Asali Da Tarihin Ba Da Sandar Sarautar

Daga Bilkisu Yusuf Ali, Kano

“SAI KA YI”

Kalaman da suka yi fice a bakunan Kanawa kenan a lokacin da ya ke riƙe da sarautar hakimci. Fata nagari lamiri, ya tabbata ga Sarkin Kano na 15, Alhaji Aminu Ado Bayero, don a gobe Asabar, ranar 3 ga Yuli, 2021 ne Gwamnatin Jihar Kano ta ware da ƙawata ranar na yin mashahurin taron da aka jima ba a yi irinsa ba, don bayar da sanda, duba da tun gabanin taron Jihar Kano ta yi cikar kwari a kowanne ɓangare ka duba, on bikin bayar da sanda. Alaƙar Sarkin na Kano da sarakunan Nijeriya, musamman Arewa ya sa sarakunan shirin mayar da kaɓakin alheri da alheri.

Asalin Sandar Mulki

Ita wannan sanda an samo asalin bayar da ita ne bayan zuwan Turawan mulki Ƙasar Hausa. Turawa sun samu dukkan limaman Ƙasar Hausa a wancan lokacin su na amfani da kandiri (wato sanda) suna dogarawa, musamman yayin huɗubar Juma’a. Wataƙila, wannan ya ba su haske wajen assasa da sanin muhimmancin sanda. Miƙa sanda na nufin shiga ofis a hukumance da fara aiki gadan-gadan.

Masarautar Kano tana cikin manyan masarautu a Ƙasar Hausa cikin yankin Yammacin Afrika. Tarihi ya nuna cewa, tsohuwar masarauta ce da aka kafa shekaru aru-aru tun kafin zuwan addinin Musulunci yankin Ƙasar Hausa. Birnin Kano ya kasance cibiyar kasuwanci a yankin Arewacin Nijeriya da Jamhuriyar Nijar da ke maƙwabtaka da birnin.

Kafin zuwan Turawa babu Sarki Mai Daraja ta ɗaya, babu wani bambanci tsakanin sarakuna, sai dai a Daular Sakkwato an amince Sarkin Musulmi shine jagora. Amma da Turawa suka zo sun raba garuruwan da suka mamaye zuwa larduna, kuma kowanne lardi yana ƙarƙashin Sarki Mai Daraja ta Ɗaya da kuma wasu sarakunan darajoji hawa-hawa.

Wane Ne Sarkin Fulani Na 15 A Kano, Aminu Bayero?

Tun daga kan sarki Sulaimanu (Sarki na farko a Daular Fulani a Kano) har zuwa kan SarkiAdo Bayero babu inda Sarki Aminu ya kauce wa hanyar magabantansa ta tsarin addini da sarauta. Sarki ne da ya tsaya kuma ya tsayu kan kare martabar Gidan Dabo da jikinsa da ruhinsa. Babbar shaidar ita ce, da bakin duk wanda za a tunkara a cikin Kano ba ta saɓawa cewa, shi ne Haƙuri. Wannan shaidar ita ce, mafi kyawun shaida da ɗan-adam ke fatan samu, domin ko mahaifinsa, Marigayi Dr. Ado Bayero, ita ya samu.

A inda ya tashi a unguwar Gwangwazo, abokansa da waɗanda ke ƙasa da shi, kowa ya shaide shi da rashin girman kai, kai ka ce ba Ɗan Sarki ba ne, saboda yadda ya ke ta’ammali da ’ya’yan talakawa. Alhaji Aminu Ado Bayero tunda ya tashi mutum ne na mutane; babbar shaida shi ne yadda mutane ke goyon bayansa yayin da ya fito Hawan Sallah.

Taƙaitaccen Tarihin Sarkin Fulani Na 15 A Kano

An haifi Mai Martaba Sarkin Kano na 15 a zuriyar Fulani a cikin ƙwaryar Kano ranar 21 ga Agusta, 1961, kafin a naɗa mahaifinsa, Marigayi Alhaji Ado Bayero, da shekara biyu a matsayin Sarkin Kano. Ya yi karatu a makarantar firamare ta Ƙofar Kudu. Ya yi sakandire a makarantar sakandire ta kwalejin gwamnati ta Birnin Kudu.

Bayan ya kammala ya je Jami’ar Bayero, inda ya karanci aikin jarida da kimiyyar siyasa, ya kammala digirinsa a nan, ya yi hidimar qasa a jihar Biniwai, inda ya yi aiki a gidan talabijin na ƙasa.

Ya fara aiki a kamfanin jirage na Kabo Air a matsayin jami’in hul]a da jama’a daga shekarar 1985 zuwa 1990, inda ya riqi har matsayin darakta.

Batun abin da ya gada kuwa wato Sarauta, Alhaji Aminu Ado Bayero, ya fara shiga sha’anin mulki tun yana da }ananan shekaru. Ya fara tun a shekarar 1990, inda mahaifinsa, Mai martaba Sarkin Kano Marigayi Dr Ado Bayero, ya ba shi sarautar Ɗanmajen Kano kuma Hakimin Nassarawa. Ya samu canji, inda ya koma Danmajen Kano kuma Hakimin Gwale a shekarar 1991. Likkafa ta ci gaba, inda ya zama Turakin Kano kuma Hakimin Dala na tsahon shekara goma.

A shekarar 2001 ya zama Sarkin Dawakin Tsakar Gida. Ya na zaune a wannan kujerar har zuwa 2014 yayin da Sarkin Kano Muhammadu Sunusi II ya naɗa shi sarautar Wamban Kano kuma ɗan Majalisar Sarki, sarautar da ya riƙe har watan Disamba na shekarar 2019, inda Gwamnan Jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya gididdiba Masarautar Kano zuwa sarautu biyar kuma ya naɗa Alhaji Aminu Bayero Sarkin Bichi na farko.

Likkafa ta ci gaba a ranar 10 ga Maris ɗin shekarar 2020, ranar da gwamnan ya naɗa shi Sarkin Kano kacokam bayan yi wa Sarkin Fulani na 14, Muhammadu Sunusi II, murabus.

Kasancewarsa A Karagar Mulki

Haƙiƙa kasancewar Alhaji Aminu a sarautar karagar Sarkin Kano bai zama abin mamaki ba, don ta kowanne ɓangare ya gada. Ya gada ta ɓangaren mahaifiya da mahaifi. Sannan kuma wancan fata nagari lamiri da Kanawa ke yi masa na “SAI KA YI” alama ce da ke nuni da cewa, karɓaɓɓe ne a cikin al’ummarsa. Don haka za a iya cewa, zamansa sarki abu ne da ake sa rai kuma ake jira kawai, kuma Allah ya tabbatar.

Samun kansa a tsaka mai wuya lokacin siyasa da yadda ya riƙe sarautar ya ci gaba da gabatar da ayyukansa na fada cikin mutunci da girmamawa shi ma abu ne da wanda duk ya san Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado ya san ba zai ƙetare wannan ba, don kuwa shi jininsa a cuɗe yake da iya mulki da shugabanci da dattako da kunya da kawaici wanda ya gada tun daga sarki Dabo.

Biyayyarsa ga mahaifinsa Sarkin Kano Ado Bayero ya ba shi tabarrakin ƙana’a da mutunta ɗan-adam da sanin girman na gaba.Wannan ta ƙara masa farin jini da ƙauna ga al’ummar jihar Kano don suna kallon Alhaji Aminu Ado Bayero tamkar mahaifinsa.

Manhaja na taya Alhaji Aminu Ado Bayero murna. Tabbas laya ta yi kyan rufi, ya gaji halin Dabo, ya gaji halin Bayero! Allah ya sa ya yi jinkiri da ƙarko da mutunci da haiba irin na mahaifinsa, Marigayi Alhaji Dr. Ado Bayero, wanda ya ɗauki hanya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here