SARKIN DAURA A KAMFANIN SHINKAFA NA FARKO A DAURA

Daga Suleman Harris daura
A ranar Litinin 11/1/2021 Mai martaba sarkin Daura Alh. (Dr.) Umar Farouq Umar ya kai ziyara ta musamman zuwa kamfanin shinkafa (RIJMA PARBOILED RICE) .
Wanda yake a Daura kan hanyar Kongolam GRA Daura kusa da gidan man Dan Marna kamfanin Shugaban kamfanin ALAS ya bude wato Alh. Lawal Sulaiman ALAS
An bude shine don samar da shinkafa a cikin kasa a bisa kudirin gwabnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta Samar da wadataccen abinci a cikin kasa Najeriya.
Sarkin Daura ya yaba da kokarin mai kamfanin domin yin wannan babban aiki da kawo cigaba a cikin Masarautar Daura tare da samawa matasa aikin yi. Daga karshe kuma yayi addu’a da fatan alkhairi. Ga hotunan ziyarar

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here