Sarki Salman na Saudiyya ya kira Shugaba Buhari ta waya

Copyright: Saudi
Sarki Salman bin Abdulaziz na Saudiyya ya kira Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ta waya, kamar yadda kamfanin diilancin labarai na Saudiyya ya bayyana.
Shugabannin biyu, sun tattauna ne kan ƙawancen diflomasiyya tsakanin ƙasashen biyu da kuma hanyoyin da za a bi na haɓaka yarjeniyoyin da ke tsakanin ƙasashen biyu.
Ko a watan Agusta sai da Sarki Salman ɗin ya kira shugaban Najeriyar domin tattaunawa kan hanyoyin da za a daidaita kasuwar man fetur a duniya.