Sarki Muhammadu Sanusi ya jagoranci Sallar Idi a Kaduna

Muhammadu Sanusi a Kaduna

Mai Martaba tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi na biyu ya jagoranci Sallar idi a Kaduna tare da Gwamna Nasir el-Rufa’i na jihar.

Gwamna El-Rufa’i ne ya wallafa hotunan yadda Sallar Idin ta kasance a Masallacin Idin Murtala Square.\

Ya kuma wallafa saƙon barka da sallarsa ga al’ummar jihar Kadunan inda ya taya su murnar zagayowar wannan rana.

Sannan ya yi kira ga mutane da su yi addu’a ga jihar da ƙasar baki ɗaya a wannan yanayi mai wahala da ake ciki kamar yadda sanarwar ta ce.

Ga dai wasu hotuna na yadda sallar ta kasance.

Sallar Idi a Kaduna
Sallar Idi a Kaduna
Sallar Idi a Kaduna

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here