Me ya sa ake cewa Sarkin Katsinan Maradi

Kamar yadda bayani ya gabata kan tushen Maradi, Masana sun ce wadanda suka gujewa jihadin Danfodio ne suka kafa Masarautar Maradi.

Kuma duk da cewa asalin Maradi wani yanki ne na ƙasar Katsina ta Najeriya, amma masarautar ta fice ne daga ƙarni na 19.

“Wasu Katsinawan Maradi a Nijar har yanzu suna ganin Katsina ta Najeriya yanki ne na masarautarsu,” in ji Farfesa Ado.

Ya ce tun da Katsina ta rabu biyu, sai gidan sarautar Korau ya baro birnin Katsina ya dawo ya kafu a Maradi – “Shi ya sa ake cewa Sarkin Katsinan Maradi ko Katsina ta arewa ko katsina ta Faransa.”

Issoufou Magagi ya ce Korau ne ya kafa Daular Katsina ta biyu, baya ga Daular da Komayau ya fara kafawa a karni na shida wanda ya fara kafa daular Katsinanawa a shekarar 1665.

“Muhamman Korau wanda shi ne asalin Daular Katsinan Maradi ya kafa daularsa ne a 1348. Sannan Ɗan Ƙasawa ya kafa Daular Katsinan Maradi a 1820, wacce ita ce Daular Katsinawa ta uku,” in ji shi.

Farfesa Ado ya kuma ya ce Maradi tana karkashin masarautar Katsina ne tun kafin jihadi ba ma kafin zuwan turawa ba wato kafin shekara ta 1807 lokacin da goguwar jihadi ta ci Katsina.

Kamar yadda ake cewa “Katsinawa jikokin Korau – To ƴan gidan Korau ne suka taso suka dawo Maradi.”

Don haka a cewar Farfesa Ado, Maradi wani yanki ne na Katsina – Kuma Maradi da Aguie da Madarounfa da Tessaoua da Dakoro da Korgom da Kanan Bakache duka yankuna ne na Katsina kafin goguwar jihadi ta raba su.

Sai dai ya ce gidan sarautar Maradi ne ya kafa Daular Katsina a karni na 15 bayan saukar Durɓawa wanda ya ba birnin Katsina kofofinta kamar kofar Ƙwaya da Ƙofar Ƙaura da Ƙofar Guga da kofar Marusa.

“Shi ne ya mayar da Katsina Sarkin Kasuwa, ya ba ta jami’o’inta kamar jami’ar Ɗan Masani da ta Ɗan Marina da ta Ƴan Doto wadda babbar jami’ia ce a Afirka duk da cewa yanzu babu ta.”

Malam Issoufou Magaji ya ce ana cewa Katsinan Maradi don a bambanta da Katsina ta Najeriya wato Katsina ta ƙaya da Katsina ta Maradi ta Nija

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here