Abubakar Bukola Saraki, shugaban majalisar dattawa na Najeriya ya bayyana gaskiyar abin da ya faru lokacin da ya kasance a hukumar EFCC da yammacin jiya Asabar, 31 ga watan Yuli, 2021.

Saraki, ya bayyana cewa, ba kama shi aka yi ba, kawai dai ya kai kansa ne domin fayyace wasu batutuwa da suka taso game dashi.

Cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Facebook, dauke da sa hannun Yusuph Olaniyonu, na ofishin yada labarai na Saraki ya bayyana cewa, Saraki ya kai kansa ofishin EFCC da son ransa, kuma ba kama shi aka yi ba.

Da yake bayyana wani batu, wani yankin sanarwar ya ce:

“Za a tuna cewa daidai da umurnin Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja kan karar Hakkin Dan Adam da Dakta Saraki ya shigar a lokacin tsohon Shugaban Hukumar EFCC wanda ya hana hukumar binciken sa har sai an warware lamarin.

“Hukumar a zaman ta na karshe a ranar 14 ga Yuli, 2021, ta roki alkalin cewa umurnin yana hana su yin aikin su.

“Bayan wannan korafi, Dakta Saraki, a matsayinsa na dan kasa mai rikon amana, a cikin son ransa ya tunkari hukumar a farkon lokacin da ya dace, cikin shiri ya ziyarci ofishin hukumar tare da fayyace dukkan batutuwan da za su so su gabatar.

“Don haka, ya ziyarci ofishin hukumar a yammacin yau kuma ya amsa wasu tambayoyi.

“Dakta Saraki ya kuma tabbatar wa da hukumar cewa ba shi da abin da zai boye kuma a ko yaushe zai mika kansa don fayyace duk wasu batutuwa da ka iya bukatar bayaninsa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here