Saraki ya bai wa Buhari shawara kan rikicin makiyaya da Yarbawa

Tsohon shuagaban majalisar dattawan Najeriya Abubakar Bukola Saraki ya shawarci shugaba Buhari kan rikicin da ke kara ruruwa tsakanin makiyayay da Yarbawa a yankin kudancin kasar.

Cikin wasu jerin sakonnin da ya wallafa a shafinsa na Twitter Saraki ya ce yana bibiyar duka abubuwan da ke faruwa game da wa’adin da aka bai wa Fulani makiyaya a Jihohin Oyo da Ondo, wanda ya kai da kona duniyoyinsu a jihar Oyo.

Ya shawarci Shugaba Buhari da ya kira dukkan masu ruwa da tsaki daga bangarorin biyu da kuma bangaren tsaro domin yi wa tufakar hanci tun kafin ta yi kamari.

Ya kara da cewa wannan ba lokacin da za a tsaya ana maganar jam’iyyar APC ko PDP ba ne, lokaci ne da za a ceto Najeriya daga duhun da take neman fadawa.

Ya kuma ambato shugaban Majalisa Ahmed Lawal da mataimakinsa Femi Gbajabiamila da su tabbatar majalsia ta shiga cikin wannan lamari.

Ya ce halin da ake ciki na tsaro a Najeriya kowa na da ta cewa domin neman mafita.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here