Sanatocin Najeriya sun sake buƙatar Buhari ya sallami manyan hafsoshin tsaro

...

Majalisar Dattawan Najeriya ta buƙaci Shugaban ƙasar Muhammadu Buhari ya sallami manyan hafsoshin tsaro na ƙasar.

Hakan na zuwa ne bayan Sanata Kashim Shettima ya gabatar da wani kudiri gaban majalisar na ɗaukar mataki mai tsauri bayan kashe manoma 43 a jihar Borno.

A na shi ɓangaren, Sanata Adamu Aliero, ya ƙalubalanci Shugaba Buhari kan rashin zuwa Borno domin yi wa jama’ar jihar jaje.

Wannan kudurin na Kashim Shettima irinsa ne na biyu a cikin watanni shida, inda ko a kwanakin baya sai da sanatocin suka buƙaci Shugaba Buhari ya sallami shugabannin tsaron.

Social embed from twitter

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here