Sanata Ahmad Babba Kaita, Hon. Jamil Sadauki, Shugaban Jam’iyyar PDP, Majigiri da sauran jigajigan jam’iyyar PDP sun hadu sun tattauna da tsohon Gwamnan jihar Katsina, H.E Barrister Ibrahim Shema a Abuja.

Sanatan shiyyar Katsina ta yamma, ya shigo jihar Katsina a yau Talata inda ya gana da shugabannin jam’iyyar PDP na jihar Katsina, daga bisani suka dunguma suka tafi Abuja don ganawa da Gwamna Shema.

Tattaunawar tasu ta ta’allaka ne kan makomar sanatan a siyasance, kamar yadda Katsina Post ta samu.

Ana saran cewa Sanata Babba Kaita zai fidda sanarwar komawa jam’iyyar jam’iyyar PDP nan bada jimawa.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here