Sanata Sadiq Yar’adua Ya Kaddamar Da Takarar Sa Ta Kujerar Gwamnan Jihar Katsina A Helkwatar Jami’yyar APC

Sanata Sadiq Yar’adua ya jagoranci dumbin magoya bayan sa zuwa hedikwatar jam’iyyar APC ta jihar Katsina a ranar Talata inda ya bayyana mata aniyar sa ta nan tikitin takarar kujerar Gwamnan jihar Katsina na jam’iyyar.

Da yake jawabi a hedikwatar jam’iyyar, Sanata Sadiq Yar’adua wanda ya wakilci mazabar dan majalisar dattawan shiyyar Katsina ta tsakiya daga shekarar 2011 zuwa 2015 ya bayyana dalilin sa na shiga takarar da cewa don ya ceto jihar Katsina daga kangin talauci da matsalar tsaro.

Sanata Yar’adua ya kara da cewa tabbas jihar ta Katsina na bukatar gogagge kuma jajiryaccen shugaba da ya san tattalin arzikin kasa ya kuma goge a fagen siyasa da mulki a zabe mai zuwa shiyasa ma ya gabatar da kan sa ga jam’iyyar domin ta ba shi tikitin takarar.

Haka zalika duk dai a hedikwatar jam’iyyar, Sanata Yar’adua ya ja hankalin shugabannin jam’iyyar na jiha a dukkan matakai da kuma wakilan da ke yin zaben fitar da gwani da su ji tsoron Allah su kuma kamanta adalci a wurin fitar da ‘yan takarar jam’iyyar a dukkan matakai.

Sanata Yar’adua wanda ya bayar da tabbacin bi da kuma mika wuya ga dukkan wanda ya lashe zaben fitar da gwani na jam’iyyar idan har aka yi adalci ya kuma sha alwashin jagorantar ya’yan jam’iyyar wajen tabbatar da adalci idan har ya fahimci akwai rashin adalci a cikin tsarin fitar da ‘yan takarar.

A na shi jawabin, sakataren jam’iyyar ta APC na jiha, Alhaji Shitu S. Shitu ya yabawa kokari da jajircewar dan takarar tare da bayyana shi a matsayin wanda yayi silar zaman sa cikin shugabancin jam’iyya tun asali.

Haka zalika Malam Shitu ya bayar da tabbacin cewa jam’iyyar za ta yi adalci ga dukkan ya’yan ta da suka fito takara ba ma na kujerar Gwamna kadai ba har ma a dukkan kujeru.

Tun da farko Shugaban jam’iyyar APC na jihar Katsina, Alhaji Sani Ali Daura ya yi ma dan takarar barka da zuwa hedikwatar jam’iyyar tare da bayar da takaitaccen tarihin gwagwarmaya da kuma gudummuwar da ya bada wurin kafuwar jam’iyyar.

Daga bisani Sanata Sadiq Yar’adua ya gudanar da taron yan jarida inda ya bayyana manufofi da kudurorin sa ga jihar Katsina idan Allah ya ba shi nasara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here