Advert
Home Sashen Hausa Sanata Mandiya Ya Samar da Wutar Lantarki A Babban Asibitin Funtuwa

Sanata Mandiya Ya Samar da Wutar Lantarki A Babban Asibitin Funtuwa

Daga Abdulrashid Musa

A ranar Alhamis 18/11/2021 ne, aka kaddamar da aikin samar da wutar lantarki mai amfani da hasken rana a babban asibitin garin Funtuwa a Jihar Katsina da nufin taimakawa wajen kula da marasa lafiya.

Wannan aiki na cikin manyan ayyukan raya kasa da Sanata mai wakiltar Shiyyar Funtuwa, Sanata Bello Muhammad Mandiya ya gabatar domin jama’ar yankin su amfana da romon dimokradiyya.

Baya ga samar da hasken wutar lantarki mai amfani da hasken rana a babban asibitin garin Funtuwa, akwai kuma aikin yashe madatsar ruwa da ke garin Funtuwa, gami da sabunta wasu injinan da ke cikinta.

A wani bayani da ya raba wa manema labarai, mataimaki na musamman ga Sanata Bello Mandiya, Mubarak Dabai ya raba wa manema labarai, ya bayyana cewa, akwai aikin wata doguwar hanya wadda take cikin garin Malumfashi da kuma aikin gyaran bai-daya da aka yi a asibitin mata da yara da ke garin Malumfashi da dai sauransu.

A lokacin kaddamar da wadannan ayyukan alherin da aka Sanata Bello Muhammad Mandaya ya samar, Jagoran tawagar, Garkuwan Kudun Katsina, Alhaji Abdul’aziz Lawal Dan Yari, ya bayyana matukar gamsuwarsa da wannan ci gaban da suka samu a Shiyyar tasu.

A lokacin da ake kaddamar da wadannan ayyukan, Alhaji Dan Yari, ya bayyana munufar Sanata Mandaya na kirkiro wadannan ayyukan alherin da kuma wadanda yake nufin gudanarwa nan gaba a Shiyyar Funtuwa.

“Sanata Bello Muhammad Mandiya ya samar da wutar lantarki a babban asibitin garin Funtuwa, domin ganin an kawar da wahalar da ake sha wajen samar da wuta a babban asibitin, inda aikin samar da wutar zai taimaka wajen inganta harkar lafiya a babban asibitin”, in ji shi.

Da yake tsokaci a kan aikin samar da ruwan sha kuwa, Alhaji Alhaji Abdul’aziz Lawal cewa ya yi; “Tun da aka gina madatsar ruwa ta Funtuwa ba ta taba samun kulawa ta wani gyara ba sai zuwan Sanata Bello Mandiya. Saboda haka mu a Shiyyar Funtuwa za mu ce kwalliya ta biya kudin sabulu”.

Mutane da dama ne suka tofa albarkacin bakinsu a lokacin da ake kaddamar da aikace-aikacen. Daga cikinsu akwai Uban Kasa, Sarkin Maska, Hakimin Funtuwa, Alhaji Sambo Idris Sambo da dai sauransu.

Bugu da kari tawagar ta zagaya, tare da duba wasu ayyukan alheri da Sanatan Mandiya yake gudanarwa, wa]anda suka hada da na gina wasu azuzuwan karatu guda shida a makarantar Sakandire ta ’yan mata da ke Karamar Hukumar Kafur da duba aikin wata magudanar ruwa duk dai a cikin garin na Kafur.

Sai kuma wasu daga cikin ayyukan samar da ruwan sha a garin Bakori, tare da duba aikin daben kasa a babbar kasuwar Malumfashi da dai sauransu.

Daga cikin ’yan rakiyar Wakilin Sanatan, akwai mataimakin Shugaban jam’iyyar APC na Shiyyar Funtuwa, Alhaji Ibrahim Danjuma Malumfashi, Alhaji Ibrahim Bala Funtuwa, Mansir O. O. da matasa maza da mata ’yan siyasa da dai sauransu.

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

THE FEDERAL MORTGAGE BANK OF NIGERIA (FMBN) HAS MADE HISTORY UNDER THE BUHARI ADMINISTRATION!

#PositiveFactsNG Do you know that ever since the Federal Mortgage Bank of Nigeria (FMBN) was established about 25 years ago, its greatest record of achievement...

YANZU-YANZU | Jirgin ruwan Bagwai dake jihar Kano mai dauke da fasinjoji 40 Yayi hatsari

Jirgin ruwan wanda ya debo dalibai mata da maza daga garin Badau zuwa garin Bagwai a jahar Kano yayi hatsari a cikin ruwan Yanzu...

ALLAH SARKI: ALLAH KA RABA MU DA RANAR NADAMA

Danjuma katsina  @Katsina City News A shekarar 2000 na dawo Katsina da zama, bayan shekaru na gwagwarmaya da tsallake siratsai kala-kala. Bayan na dawo na tsara...

Yadda Kotu Ta Ruguza Zaɓen Bangaren Ganduje Na Jam’iyyar APC

Wata babbar kotun Abuja ta soke zaben shugabannin jam'iyyar APC bangaren gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje. Alkalin kotun Hamza Muazu ya haramta zaben da...

EFCC Charges Corps Members To Take CDS More Seriously

The Port Harcourt Zonal Commander of the EFCC, Assistant Commander of the EFCC, ACE Aliyu Naibi has called on members of the National Youth...