Advert
Home Sashen Hausa Sanata Babba Kaita Ya Lashe Zaɓen Fidda Gwani na Sanatan Shiyyar Daura

Sanata Babba Kaita Ya Lashe Zaɓen Fidda Gwani na Sanatan Shiyyar Daura

Jam’iyyar PDP ta ayyana Sanata Ahmed Babba Kaita a matsayin Ɗan Takarar daya Lashe Zaɓen Fidda Gwani na Shiyyar Daura a Ƙarƙashin jam’iyar.

Sanata Ahmed Babba Kaita wanda ya yi takarar ba tare da abokin hamayya ba, Jam’iyyar ta ayyana shi bayan dukkanin Masu Kaɗa ƙuri’a Delegates sun jefa ƙuri’ar amince wa da Takarar tashi, a wani taro daya wakana a Sakatariyar PDP ta Shiyyar Daura.

Taron ya samu halartar wakilan Jam’iyyar PDP na Ƙasa, da na Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta INEC, da Ƴan Takarkari na Shiyyar Daura, gami da Ɗan Takarar Gwamnan a Jam’iyyar PDP Alhaji Salisu Yusuf Majigiri.

Haka zalika Taron ya samu halartar Ɗumbin Magoya bayan Sanata Ahmed Babba Kaita wanda suka yi dafifi a ciki da wajen sakatariyar domin ƙara jaddada mubaya’a da goyon bayan su ga Ɗan Takarar Sanata Ahmed Babba Kaita.

Dayake jawabi jim kaɗan bayan Jam’iyyar PDP ta ayyana shi a matsayin Ɗan Takarar Kujerar Sanata, Ahmed Babba Kaita ya godema masu zaɓe-Delegates da Suka ga ya cancanta suka zaɓe shi domin ya ƙara wakiltar su a Majalisar Dattijai ta Ƙasa a ƙarƙashin Jam’iyar PDP.

Ahmed Babba Kaita yace tun lokacin da ya dawo Jam’iyyar yake ganin irin soyayya da goyon bayan Al’umma da suke cigaba da nuna masa, sai ya sha alwashin cigaba da kawo ɗumbin ayyukan cigaba idan aka sake zaɓen shi a Shekarar 2023.

Ya yi addu’a ga Allah daya baiwa Jam’iyyar PDP nasara tun daga matakin Ɗan Majalisar Jaha har zuwa Shugaban Ƙasa, domin Ƙasar ta cigaba da shaida ɗumbin ayyuka cigaba.

“Ina kira ga Ƴan Takarar da suka samu nasara da waɗanda suka faɗi a zaɓen fidda Gwani, da su kasance masu haƙuri, tare da bada goyon bayan su domin nasarar Jam’iyyar a 2023”. Inji Sanata Kaita

A nashi Jawabin, Ɗan Takarar Gwamnan Jahar Katsina a Jam’iyyar PDP Alhaji Salisu Yusuf Majigiri yayi kira ga masu kaɗa ƙuri’a Delegates, dasu kasance masu zaɓen Ɗan Takarar da zasu yi alfahari dashi idan ya lashe zaɓe a Shekarar 2023.

Alhaji Salisu Yusuf Majigiri yace Jam’iyyar PDP a shirye take idan ta samu nasara ta tabbatar ta kori yunwa da APC ta kawo ta hanyar tsare-tsaren na wahalhalu data ƙaƙabawa Ƴan Ƙasar.

Alhaji Salisu Yusuf Majigiri ya hori Al’umma dasu duba cancanta su zaɓi nagartattun mutane, musamman wanda Jam’iyyar ta kawo masu domin cigaba da kurɓar romon Dimokuraɗiyya.

Wakilin Jam’iyyar PDP na Kasa wanda kuma shine Sakataren Zaɓen Sanatan yace, Ahmed Babba Kaita shine Ɗan Takara ɗaya tilo da bashi da abokin hamayya da Jam’iyyar ta saida wa Tikitin Tsayawa Takara a Ƙasar nan.

Yace sakamakon rashin abokin hamayya da kuma kaɗa kuri’ar amince wa da Delegates Suka Yi, a don haka, Jam’iyyar ta ayyana shi a matsayin wanda ya lashe Zaɓen Fidda Gwani na Jam’iyyar.

KATSINA CITY NEWShttps://www.katsinacitynews.com
Danjuma Katsina, Dan Jarida, Manazarci, Marubuci, Mamallakin Jaridun KATSINA CITY NEWS, JARIDAR TASKAR LABARAI, THE LINKS NEWS, a karkashin Kamfanin MATASA MEDIA LINKS NIGERIAN LTD

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Must Read

NIMET Installs Message Dissemination Platforms At Abuja, Kaduna, P/H Airports #Positivefacts

https://www.facebook.com/101788642037662/posts/pfbid02SkXT7vgAdTkuHz5gW6EaSFt3qZoc4hVMtBMXRMw6SzFv1da5ujPAsEmWyd535tYgl/ Nigerian Meteorological Agency (NiMET) has procured and installed seven automatic message dissemination platforms at Abuja, Kano, Lagos, Maiduguri, Kaduna, Enugu, and Port Harcourt airports. The...

FISHERIES PROJECT CREATES JOBS TO OVER TEN MILLION NIGERIAN #PositivefactsNG

https://www.facebook.com/101788642037662/posts/pfbid0Gc6v3B4e1KT8u7qGbmcMUofbzSaejnB1PTcdjHrBSUaUtQA28bQNeQ3qgLAnhBfzl/The federal government under the leadership of president Muhammadu Buhari, GCFR, has create over ten million jobs to Nigerian through fisheries project, the honourable minister...

Muna kira ga Gwamnati ta taimaka mana kada ruwan damuna ya share mana gidaje….. Mutanen Unguwar Ɗoroyi a cikin garin Katsina.

Muna kira ga Gwamnati ta taimaka mana kada ruwan damuna ya share mana gidaje..... Mutanen Unguwar Ɗoroyi a cikin garin Katsina. Zaharaddeen Ishaq Abubakar @Katsina...

Yunƙurin Ficewar Sanatoci 20 Daga APC: Ku Nemawa Kanku Mafita Tun Kafin Wuri Ya Kure Maku – Hon. Ɗanlami Kurfi

Kamar yadda rahotanni ke cewa akwai kusan Sanatoci 20 na jam'iyyar APC da ke kokarin ficewa daga jam'iyyar saboda wasu dalilai da suka ƙi...

MATSALAR TSARO: Yanda Al’umar garin Mada, dake ƙaramar Hukumar mulkin Gusau suke barin gidajen su…

Matsalar Tsaro: Yadda al'umar garin Mada dake karamar hukumar mulkin Gusau ta jihar Zamfara ke barin matsugunnansu a safiyar yau Asabar sakamakon ta'azarar hare-haren...
%d bloggers like this: