Gwamna Aminu Bello Masari ya bayyana cewa samun taimako na kai tsaye ga manoma ta hannun gwamnatocin jiha kananan hukumomi zai taimaka kwarai wajen habaka noman, ta yadda aikin gonar zai zama kasuwanci ga manoman ba kawai hanyar samar da abinci ba.

Gwamnan ya bayyana haka ne yau a Abuja, yayin da ya amshi bakuncin Daraktan kula da ofishin habaka huldatayya tsakanin Ingila da kasashen waje da kuma kasashe rainon Ingilar Dr Christopher Pycroft.

Alhaji Aminu Masari ya shaida wa Daraktan cewa jihar Katsina ba ta da wata sana’a ko aiki da yake samarwa wa al’umma aikin yi da bunkasar tattalin arziki irin noma, amma kalubalen ta’addanci ya hana mu amfana da wannan harka. Sanin cewa hakan babbar matsala ce ga al’umma, yasa ala tilas gwamnati ta dauki ‘yan kungiyar sintiri da kuma wasu da suka sadaukar da kawunan su, aka basu horo domin dafa ma jami’an tsaro wajen yakar ‘yan ta’adda.

Ganin yadda nauyin samar da tsaro ya haye ma gwamnatocin jihohi yasa suke tattaunawa da Majalisar Tarayya domin ganin anyi gyaran da ya dace ga tsarin mulkin kasar domin saita yadda lamarin samar da tsaron zai kasance.

Ta fuskar siyasa kuwa, Gwamnan ya sake jadda ra’ayin shi na mayarda mulki kudancin Kasar nan amma ba bisa tilasci ba tunda hakan baya cikin tsarin mulkin kasa ko na wata jam’iyya, iyaka dai yin haka zai kara dankon tarayya da kuma kishin kasar a zukatan al’umma.

Tun farko a jawabin shi, Dokta Pycroft ya shaida wa Gwamna Aminu Masari cewa kasar Birtaniya na shirin bullo da tsare tsare na taimaka ma manoma domin habaka sana’ar, kuma wannan shi ne makasudin ziyarar tashi, haka kuma ya bayyana aniyar shi ta kai ziyara jihar Katsina domin tabbatar da tsari ingantacce na tafiyar da wadancan shirye shirye.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here