Akalla mutane 10,000 yan asalin Jihar Katsina ne Ke aikin hakar Zinare a Kauyen Kwandago dake Jamhuriyar Nijar, Inji majiyar mu ta Fact 24.

Shi dai wannan yanki na Kwandago dake da albarkacin ma’adanin na zinare, yana a Karkashin Karamar Hukumar Dan Issa ta Jihar Maradi dake Jamhuriyar Nijar.

Yankin na Kwandago yana da iyaka da Karamar Hukumar Jibia ta Jihar Katsina,kuma yanada nisan kilomita kusan 20 daga garin Kukar Babangida dake Kan hanyar Katsina zuwa Jibia.

Wakilin The Fact 24 da ya ziyarci wannan yanki da ake aikin hakar zinarin,ya ruwaito cewar bayan yan asalin Jihar Katsina akwai sauran mutane dake aikin hakar zinarin daga wasu Jahohin Najeriya.

Kamar yadda alkalumma suka nuna,kashi 75 zuwa 80 na mutanenda Ke aikin hakar zinarin da masu kasuwanci a yankin yan asalin Najeriya ne Wanda yawansu ba zai gaza su 20,000 ba.

A lokacinda The Fact 24 ta ziyarci yankin,an samu jama’a sun tsunduma a aikin hakar zinarin wasu kuma na aikin fasa dutse a yayinda wasu kuma Ke aikin dura kasa a buhunna wasu kuma na aikin wankar dutse da kasa da aka saro daga ramukan hakar zinarin.

Har ila yau,The Fact 24 ta lura cewar wasu mutanen sun tsunduma a aikin debo ruwa a jarkoki Wanda akan sayar da shi akan kudi naira 300 kowace jarka baya ga masu daukar duwatsu da kasa zuwa wurin wanki dake Garin Dan Issa.

A halinda ake ciki dai al’umma nata yin tururuwa zuwa wannan yanki domin neman abin sakawa bakunan salatinsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here