Wani bangare na gidan yarin da ‘yan bindiga suka kaima hari

Sama Da Fursunoni 1500 ‘Yan Bindiga Suka ‘Yanta A Harin Da Suka Kai A Gidan Yarin Imo.

Wasu ‘yan bindiga a safiyar Litinin sun kai hari a gidan Yari na Owerri da ke cikin babban birnin jihar Imo tare da ‘yanta Fursunoni sama da 1500, in ji jaridar Punch.

Maharan sun kuma kone hedikwatar rundunar ‘yan sanda ta jihar Imo da ke Owerri tare da kona kusan dukkanin motocin da ke ajiye a helkwatar rundunar.

‘Yan fashin sun saki wadanda ake garkame da su a kusan dukkanin sel a sashin binciken manyan laifuka na rundunar.

Jaridar Punch ta tattaro cewa ‘yan bindigar sun fara aiki ne daga karfe 1 na dare zuwa 3 na safiyar Litinin.

Sun rera wakokin hadin kai a gidan gwamnati da ke kusa da mintuna 30 kafin su far wa cibiyoyin, in ji majiyar tsaron ga wakilinmu.

Yayin da suka kutsa kai cikin gidan yarin tare da taimakon ababen fashewa da kuma kuzari, maharan sun ce wa fursunonin da su koma gida.

Lokacin da aka tuntu6i kakakin ‘yan sanda a jihar, Orlando Ikeokwu, ya tabbatar da kai harin.

Wasu bangaren motoci da maharan suka kona a bakin gidan gyara halinka

Amma, ya tabbatar wa mutanen jihar cewa hukumomin tsaro suna kan ƙoƙari ga lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here