Salihu Tanko Yakasai na hannunmu – DSS

Salihu Tanko Yakasai

Rundunar ‘yan sandan farin kaya ta DSS ta tabbatar da kama Salihu Tanko Yakasai, tsohon mai taimaka wa gwamnan Kano kan kafafen yaɗa labarai.

Tun a jiya Asabar ne dangin Salihu suka tabbatar wa BBC kamen nasa, inda mahaifinsa Tanko Yakasai ya ce an kama shi ne lokacin da ya fita yin aski a birnin Kano kuma suka wuce da shi Abuja, babbar birnin ƙasar.

An kama Salihu ne, wanda aka fi sani da Ɗawisu, ‘yan sa’o’i bayan ya ce“idan gwamnatin APC (ƙarƙashin Muhammadu Buhari) ba za ta iya kare rayuka da dukiyoyin al’umma ba ta sauka daga mulki” a ranar Juma’a.

DSS ta bayyana cewa ita ce ta kama shi kuma take bincikrsa a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunta na ƙasa, Peter Afunanya, ya fitar a daren Asabar.

“Muna tanbbatar da cewa Salihu Tanko Yakasai na hannun Department of State Services (DSS),” a cewar sanarwar.

Ta ƙara da cewa: “Ana bincikarsa ne a kan wani abu fiye da bayyana ra’ayinsa a shafukan zumunta kamar yadda wasu ke tsammani.”

Tuni ɓangarorin al’umma daban-daban suka yi Allah-wadai da kamen nasa. Kungiyar kare haƙƙi ta Amnesty International ta yi kira ga gwamnati da ta sake shi “nan take”.

Ita ma jam’iyyar adawa ta PDP ta ce “wannan kamen na Salihu abu ne da ba za a yarda da shi ba kwatakwata” sannan ta nemi a sake shi ba tare da wani sharaɗi ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here