Shugaban Majalisar Malamai na Kungiyar Jibwis Sheikh sani yahaya Jingir yayi Kira da kakkausar murya ga Shugaban Kasa Muhammad Buhari da yakawo karshen Yajin Aikin Malaman jamioi, sheikh yace “Bai kamata ka bari ASUU su ci gaba da yajin aikin ba ”
Kungiyar addinin Islama a Najeriya, JIBWIS ta yi kira ga gaggauta shawo matsalar yajin aikin ASUU nan take Kungiyar ta yi wannan kiran ne ta bakin shugaban majalisar malamai, Sheikh Sani Yahaya Jingir a jiya Lahadi Kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa’Ikamatis Sunnah (JIBWIS), a ranar Lahadi, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU) da su warware sabanin da ke tsakaninsu tare da janye yajin aikin malaman na jami’a. Shugaban Majalisar Malamai na JIBWIS, Sheikh Sani Yahaya Jingir ne ya yi wannan kiran a wajen rufe taron karawa juna sani na kwanaki 29 na shirin watan Ramadan mai taken: “Shugabanci nagari da tsarin samar da tsaro ga jama’a” da aka gudanar a garin Jos.
Vanguard Hausa