Sakamakon zabe “cikakken rohoto”.

A ranar 27 ga watan Disamba na shekarar 2020 ne a ka gudanar da zaben shugaban kasa tare da na ‘yan majalisu a Ƙasar Nijar, an Kuma gabatar da zaben lahiya cikin kwanciyar hankali da lumana.

Yan takara 30 ne suka suka nemi Kujerar mulkin, saidai yan takara biyu ne suka fi fice a zaben, wato Bazoum Mouhamed na jami’iyyar PNDS TARAYYA ta masu mulki, sai Kuma Mahamane Ousmane na RDR CANJI.

Zaben dai ya dauki hankalin al’umma na cikin kasa da na waje, ganin yadda zaben yazo cike da kace-nace musamman game da takarar Bazoum wanda manyan Yan adawa ke kalubalantarsa ba takardar cikakken ‘dan kasa ba.

Kafin gudanar da zaben manazarta da masu sharhi akan lamarin siyasa sunyi hasashen cewa Bazoum ka iya lashe zaben, kasancewar babu wani babban ‘dan takara da zai iya karawa dashi. To Amma lamarin sai yazo a kasin hakan, saboda kuri’un da ta samu basu isa subashi nasarar lashe zaben ba.

Ga Sakamakon yadda ya kasance :
Bazoum Mouhamed : 39.33%
Mahamane Ousmane : 16.99%
Sauran jam’iyyau kuma : 43,68%.

Tuni dai Hukumar shirya zabe ta kasa wato CENI ta sanar da zuwa zagaye na biya na wannan zaben tsakanin BAZOUM MOUHAMED da MAHAMANE OUSMANE, wanda za’a gudanar a ranar 21 ga watan fabraru na wannan shekarar ta 2021 in Allah ya yarda.

To ko meye ra’ayinku game da sakamakon zaben ? Kuma ya kuke hasashen eata kaya a zagayen na biyu ?

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here